27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Dan kasar Brazil din da yake wa kansa allurar “mai” don ya murde ya sheka lahira

LabaraiDan kasar Brazil din da yake wa kansa allurar “mai” don ya murde ya sheka lahira
  • A shekaru 6 da suka gabata ne aka ja kunnen Valdir Segato akan yiwuwar ya lalata wasu sassan jikinsa
  • Sai dai ya toshe kunnuwansa inda ya ci gaba da yin allurar mai don gabbansa su murde
  • An samu bayanai akan yadda ya mutu a gadon asibiti bayan ya gama korafi akan datsewar numfashinsa

Wani ma’aboci motsa jiki dan kasar Brazil kuma fitacce a kafar TikTok ya tara mabiya miliyan daya da dubu dari shida bayan ya yi wa kansa allurar mai, Daily Mail ta ruwaito.

Ya yi allurar ne don tara murdaddiyar kafada mai girman inci ashirin da uku (23 inches) kuma ya mutu ne ranar zagoyar haihuwarsa ta 55 a Ribeirao Preto.

Valdir Segato ya dade yana yi wa kansa allurar tsawon shekaru duk da hatsarinta amma bai damu ba duk saboda jikinsa ya murde.

Asali Segato dan Sao Paulo ne kuma ya gwada yin allurar ne bayan ganin yanayin surar Arnold Schwarzenegger da kuma sauran jarumai kamar na The Hulk a murde.

Ya kuma bayyana alfaharin da yake yi akan yadda kowa ya san sa a murde.

A shekaru 6 da su ka gabata ne aka ja kunnensa akan zai iya lalata halittarsa ya kuma kawo dameji ga sassan jikinsa idan ya ci gaba da yi wa kansa allurar mai.

Amma Segato ya ki amincewa da shawarar inda ya bayyana cewa yana jindadin yadda hankalin jama’a ya koma kansa kuma yana son ya kara girma.

Yadda ‘yar Najeriya ta sheka lahira bayan garzayawa gaban likita don kara girman mazaunanta

Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna poshcupcake_1, cikin alhini ta bayyana yadda kawarta, Crystabel ta mutu bayan yunkurin kara girman mazaunanta da ta yiPrewedding Nigeria ta ruwaito.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta tare da sanya hotunan mamaciyar:

“Ina son sanar da jama’a cewa wata kawara ta rasu a wannan asibitin da ke Jihar Legas, kwanaki kadan da su ka gabata bayan ta je a yi mata aiki.

“Ba wai ina shawartar kowa da ya ki zuwa a inganta masa surar jikinsa ba ne, ka yi idan kana so.

“Amma ina shawartarka da ka kiyaye zuwa wurin likitocin da ke ikirarin sun samu gogewa a kasar waje, su zo Najeriya su dinga halaka matasa.

“Bayan gama aikin, ta sanar da likitan yadda ya ke ta zubar da jini. Amma a haka ya ce babu komai zai tsaya.”

Ta ci gaba da kalubalantar iya aikinsa inda ta ce bai damu ba ko da kawarta ta bayyana masa cewa tana ta zubar da jini.

Ta ce abin ban takaicin shi ne yadda ta rasu ba tare da sanar da wani kowa a gidansu halin da ta ke ciki ba. Sai wasu kawayenta da su ka san ta yi aikin ne su ka bibiyeta daga nan aka ba su takarda cewa gawarta tana ma’adana gawa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe