31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Kungiyar Nyau da ke Malawi, Mozambique da Zambia: Su na tsafin da ‘yan sanda kansu tsoronsu su ke

LabaraiKungiyar Nyau da ke Malawi, Mozambique da Zambia: Su na tsafin da ‘yan sanda kansu tsoronsu su ke
  • Wata kungiyar asiri mai suna Chewa ta yi fice a kasashe uku makusantan juna
  • Akwai mambobinta a Malawi, Mozambique da kuma Zambia
  • An samu bayanai akan yadda har ‘yan sanda tsoron kungiyar suke

Wata kungiyar asiri ta mutanen Chewa mai suna Nyau da ke Malawi, Mozambique da Zambia ta yi fice kwarai, shafin The Tribe n Facebook ya ruwaito.

Kamar yadda ake fadi, su na da wani irin tsafi mai karfi wanda mutane da dama su ke tsoronsu.

Har ta kai ga ‘yan sanda ba sa iya dakatar da su ko kuma hukunta su idan har sun tafka wani laifin.

Wannan kungiyar na da shiga mai ban tsoro da kuma wani irin yanayi mai firgitarwa.

Ga hotunan wasu daga cikin mambobin kungiyar:

ojuju
Kungiyar Nyau da ke Malawi, Mozambique da Zambia: Su na tsafin da ‘yan sanda kansu tsoronsu su ke
secret cult 1
Kungiyar Nyau da ke Malawi, Mozambique da Zambia: Su na tsafin da ‘yan sanda kansu tsoronsu su ke

Ina neman mutum mai tsoron Allah wanda zai aureni – Inji jaruma Eucharia Anunobi

Sananniyar tsohuwar jaruma Eucharia Anunobi, ta sanar cewa a halin yanzu, tana matukar bukatar ta sami mijin aure.

Miji mai tsoron Allah take nema ido rufe

Jaridar Leadership ta rahoto jarumar ta bayyana cewa, tana bukatar cikakken mutum mai tsoron Allah, kuma wanda zai iya biyan bukatar aure, da gaggawa.

Ta bayyana hakan ne a yayin da ake hira da ita a kafar yada labarai ta BBC, wacce ake magana da harshen Igbo.

Tace :

Dan Allah ina so nayi amfani da wannan kafa, domin na shaidawa duniya cewa ina da bukatar aure da gaggawa. Ina so babban mutum ya bayyana kansa, domin ya sanya mini zobe a wannan dan yatsan nawa.

Abubuwan da nake so, sune mutum mai tsoron Allah kuma kyakkyawa.

Dole ya kasance zai iya sauke nauyin, kuma ya kasance yana da duk abin da zai amsa sunan sa na namiji. Dole ne ka zamto cikakke ta kowacce fuska, wannan shine kawai abin da zan ita cewa

Idan za’a iya tunawa, auren Jarumar ita da Charles Ekwu dai, ya mutu ne a shekarar 2009.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe