25.1 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

So makaho ne: Zukekiyar baturiya mai arziki ta zo har Najeriya inda ta yi wuff da gurgu

LabaraiSo makaho ne: Zukekiyar baturiya mai arziki ta zo har Najeriya inda ta yi wuff da gurgu
  • Zukekiyar mata mai zama a Amurka mai suna Ranti Jacobs Agbaminoja da kuma Omotayo Agbaminoja sun nuna wa duniya cewa akwai soyayyar gaskiya har yanzu
  • Ranti, wacce baturiya ce ta bayyana yadda ta fada tarkon soyayyar Omotayo wanda ya ke da matsalar kafa, hakan yasa ta zo Najeriya don aurensa
  • Masoyan sun nunawa duniya cewa yadda ake kallo kamar kudi ne tushen soyayyarsu ba gaskiya bane don jajircewarsu ta wuce misali

Bayan sun yi auren kotu a 2015, wata baturiya mai suna Ranti Jacobs Agbaminoja ta zo har Najeriya don auren saurayinta, Omotayo Agbaminoja wanda gurgu ne inda aka yi shagalin a 2022, Legit.ng ta ruwaito.

Baturiyar wacce ke da tushen Yarabawan Najeriya ta sanar da BBC News Yoruba a tattaunawar da su ka yi da ita cewa sun hadu da Omotayo ne a wata coci da ke Maryland.

Daga fara abota da juna, sai su ka fara soyayya wacce duk da hakan bata taba tambayarsa yadda aka yi ya fara amfani da keken guragu ba.

Baturiyar wacce ‘yar jarida ce ta bayyana cewa dakansa Omotayo ya sanar mata yadda lokacin yana karami aka yi masa allurar foliyo wacce tayi sanadiyyar shanye masa kafafu.

Kyakkyawar baturiya ta iso Najeriya wurin saurayin ta, tana shirin yin wuff da shi

A ranar Asabar 2 ga watan Yuli, 2022 da misalin ƙarfe ɗaya na rana, wata baturiya ‘yar ƙasar Canada, Natasha, za tayi wuff da wani angon ta ɗan Najeriya mai suna Gift.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa baturiyar wacce ta haifi yaro ɗaya ta shigo Najeriya a cikin ‘yan kwanakinnan domin haɗuwa da masoyin na ta a karon farko wanda suka haɗu a shafin Instagram shekara ɗaya da ta gabata.

An nuna bidiyon lokacin da baturiyar ta shigo Najeriya

Masoyan biyu sun fitar da wani bidiyo wanda ya nuna lokacin da baturiyar ta iso Najeriya yadda suka rungume juna cikin shaukin ƙauna.

Haka ma wani bidiyo da aka wallafa a TikTok ya nuna yadda suka fara hira kimanin shekara ɗaya da ta wuce.

A cewar bidiyon, matashin ya tura mata saƙo a Instagram, inda daga gaisuwar mutunci abu ya riƙiɗe ya koma abota inda daganan suka tsunduma cikin kogin soyayya.

Duk da sukar da tasha daga wurin masu amfani da yanar gizo kan cewa Gift kawai na amfani da ita ne domin samun katin zama ɗan ƙasar Canada, baturiyar ta cigaba da kare soyayyar dake a tsakanin su ta hanyar wallafa bidiyoyi masu kyau.

Natasha lokaci bayan lokaci tana sanya bidiyon yaron ta manhajar TikTok. Sai dai abinda baa sani ba shine ta taɓa aure ko bata taɓa aure ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe