Wani ɗan majalisar wakilai ta tarayya (APC Gombe) Abubukar Yunus, yayi zargin cewa harin gidan yarin Kuje da kuma sakin wani rukuni na fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna, ka iya zama bani gishiri in baka manja. Jaridar Daily Trust to rahoto.
Abubakar Yunus yana magana ne a lokacin wata hira a gidan talabijin na Channels TV a shirin su na ‘Siyasa a yau’ a ranar Talata.
Ƴan ta’adda sun sake sako wasu daga cikin fasinjojin
A ranar Talata, ƴan ɓindiga sun sako wasu ƙarin mutum biyar da harin jirgin ƙasan ya ritsa da su.
Ƴan ta’addan sun sace fasinjoji da dama lokacin da suka farmaki jirgin ƙasan akan hanyar sa ta zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, 2022.
Sai dai, a ranar 5 ga watan Yuli, 2022, ƴan ta’adda sun mamaye gidan yarun Kuje inda suka saki sama da mutum 800, ciki har da dukkanin mambobin Boko Haram dake tsare a gidan yarin.
Gwamnati tayi wata dibara ce kawai
Da aka tambaye shi ko akwai alaƙa a tsakanin sako mutanen na kwana-kwanan nan da kuma harin gidan yarin Kuje, sai ya kada baki yace:
A matsayina na wanda ya kwashe shekaru da yawa a majalisa, kuma mai sa ido kan lamuran tsaro, ba zan ce akwai shiri da matakan tsaro a wurin ba. Gwara na ce wani ɓangare ne na salo da dibara wanda gwamnati ta shirya yadda zata yi amfani da shi.
Ya ƙara da cewa,
Meyasa na ce haka? Kafin kai harin Kuje, shi an taɓa kai hari a gidan yarin? Shin shine karon farko da aka taɓa sanya ƴan Boko Haram a ciki? Meyasa? Kuma duk waɗannan jami’an suna wurin? Ina son nayi nuni da cewa tunda farko gwamnati tace tana da ƙarfin da zata iya jefa musu bama-bamai ta ƙwato mutanen amma sun tsoron asarar rayukan fararen hula.
A wajen mu, idan ƴan bindiga ko ƴan ta’adda suka ce sun sako mutanen da suka tsare, lallai zan nuni da hasashen cewa ƙila musayar ciniki ne, kawai da gangan gwamnati taƙi sa baki.
Yadda muka rayu a hannun ƴan ta’adda tsawon kwana 100 a tsare -Mutanen da aka sako na harin jirgin Abj-Kd
Mutanen da aka sako waɗanda harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya ritsa da su a ranar 28 ga watan Maris, sun bayyana yadda suka rayu tsawon kwana 100 a hannun ƴan ta’adda da suka ɗauke su.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com