25.1 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Gwamnatin jihar Kano ta bada umurnin a rushe gidan mahaifin Abduljabbar

LabaraiGwamnatin jihar Kano ta bada umurnin a rushe gidan mahaifin Abduljabbar
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rusa wani haramtaccen gini da akayi a cikin gidan Sheikh Nasiru Kabara ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnatin jihar kano ta ba da umarnin ne bayan bincike ya nuna cewa an daura ginin ne ba da izini ba a hukumance wanda filin ya kasance Mallakin masarautar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nabilusi Abubakar ya fitar ranar Talata a jihar Kano.
Babban Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, Baffa Ɗan’agundi, ya ce gwamnatin jihar ta kano da kuma masarautar ba su ba da izinin daura wannan ginin ba.
Yana da kyau jama’a su sani cewa ba bisa ka’ida aka daura wannan ginin ba wanda hakan ya haifar da shakku tsakanin gwamnatin jihar da masarautar.
Ana ci gaba da gudanar da bincike kuma gwamnan jihar Kano ya bayar da umarnin rusa katanga ginin tare da sanya kayan shakatawa na wasan yara yayin da sauran aka umurci a katanga sauran wurin da kungiyar Kadariyya ke amfani da su wajen yin zikiri.

“Gwamnan ya kuma ba da umarnin kafa jami’an tsaro na dindin-din a yankin don kare yara da iyaye a filin wasa, Domin hana haramtattun laifuka”, in ji shi.
Mista Dan’agundi kuma shi ne shugaban kwamitin kawar da haramtattun tsare-tsare.

Wata kotun Majistare ta umurci wani mutumi da ya share harabar kotun a yunkurin da ya yi na sata

Wata Kotun Majistare da ke Ota a jihar Ogun ranar Juma’a ta umurci wani matashi dan shekara 28, Abraham John, da ya share harabar kotun na tsawon kwana daya bisa laifin haurawa da yunkurin yin sata.
Mista John, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, ya amsa laifin fasa-kwaurin shiga da yunkurin yin sata.

An yankewa mai laifin hukuncin shara

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai shari’a A.O.Adeyemi, ya yanke wa mai laifin aikin yi wa al’umma hidima Na kwana daya ba tare da wani zabin tara ba.
Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Insp E.O. Adaraloye, ya shaida wa kotun cewa Mista John ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Yuli, da misalin karfe 11:40 a Ifelodun CDA, Ayetoro Itele, Ota.

Ya fasa gidan don yin sata

Mista Adaraloye ya shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya fasa gidan Popoola Kabiru da nufin yin sata.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 412 na kundin laifuffuka, na dokokin Jihar Ogun, 2006.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe