
A ranar Asabar din da ta gabata ne Amurka ta kai wani hari a jiragen yaki mara matuki in da suka kashe shugaban Al Qaeda Ayman Al-Zawahiri,a cewar shugaba Joe Biden a wani jawabi da ya yi a fadar White House a radar litinin.
CNN ta nakalto Mista Biden yana cewa “Na bada izinin a kawo karshen shi gaba daya.
Mista Zawahiri, wanda ya cika shekara 71 a duniya, ya kasance likitan kuma makusanci ga Osama bin Laden.
A cewar Mista Biden, Mista Zawahiri “yana da hannu sosai a harin 9/11, wanda harin ya jawo asarar mutane 2,977 a kasar Amurka. Shekaru da dama, ya na daga cikin wadanda suka shirya kai harin kan Amurkawa.”
“Yanzu an tabbatar da adalci shugaban ta’addanci an kauda shi.Duniya bata bukatar sake jin tsoron wani mugun mai kisa,” ya kara da cewa.
Shugaban na Amurka ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da kare ‘yan kasarta daga cutarwa kuma za ta fitar da duk wanda ya yi mata barazana ba tare da la’akari da tsawon lokacin da ta dauka ba.
Hukuncin kisa na Mista Zawahiri ya zo ne shekaru 11 bayan da Amurka ta kashe Osama bin Laden.
Ya kasance a cikin garin Kabul inda yake tare da iyalinsa wani babban jami’in gwamnatin ya bayyana kisan nasa a matsayin “daidaitaccen harin sama” ta amfani da makamai masu linzami guda biyu na wuta.
An kai harin ne a ranar Asabar da misalin karfe 9:48 na dare. Biyo bayan izinin Mista Biden makonni bayan ya gana da majalisar ministocinsa da manyan mashawarta.
Babu wani jami’in Amurka da ya ke wurin a lokacin da aka kai harin, in ji wani jami’in.
DA DUMI-DUMI: An kama wasu mutane 4 da ake zargin da hadin bakin su a harin da aka kai gidan yarin Kuje
An kama wasu mutane hudu da ake zargi da sakin bayanai ga ‘yan ta’adda game da wuraren da sojojin Najeriya ke hidima da kuma zirga-zirga a wajen Abuja.
Wani jami’in leken asirin da ya bayyana kamun ga Jaridar PR Nigeria, ya ce tuni masu laifin suna hannun wata hukumar tsaro a Abuja.
A cewar jami’in ‘yan sandan, an kama wadanda ake zargin ne da nagartattun kayan aiki da suka hada da na’urar wayar,revolver, wukake, da layu, da kuma tsofaffin wayoyi na kasar Sin, wadanda ba sa amfani da data.
Majiyar wadda ta kasance cikin tawagar da su ka kai samamen ga masu fitar da bayanan, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi don sanin masu daukan nauyin su.
Majiyar ta kara da cewa ayyukan masu kai bayanai ga ‘yan ta’adda sun hada da hare-haren da aka kai baya-baya nan a, babban birnin tarayya, FCT.
A halin yanzu dai ana ci gaba da yiwa wadanda ake zargin tambayoyi domin tantance ko suna aiki da kungiyoyin ta’addanci ko ‘yan fashi da makami ko kuma wasu da ke da wata manufa.
“Zan iya sanar da ku cewa, da gangan sojoji suka ki bayar da bayanai tun bayan harin da aka kai gidan yarin Kuje, har zuwa harin da aka kai wa sojoji a titin Bwari da Zuma Rock, ya zuwa yanzu rundunar tsaron hadin gwiwa ta kashe sama da mutane 70 dauke da makamai. majiyar ta kara da cewa, wadanda suka hada da ‘yan gidan yarin Kuje da suka gudu da kuma ‘yan ta’adda.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com