24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Ina fatan ‘yan bindiga su yi garkuwa da Buhari, El-Rufai da Garba Shehu, cewar Malam Bello Yabo

LabaraiIna fatan ‘yan bindiga su yi garkuwa da Buhari, El-Rufai da Garba Shehu, cewar Malam Bello Yabo

Fitaccen malamin addinin nan na Jihar Sokoto, Bello Yabo, ya yi fatan ‘yan bindiga su yi garkuwa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Idan ba a manta ba, ‘yan bindiga sun sace fasinjojin jirgin kasa da ya taho daga Kaduna inda suka saki wani bidiyo yayin da suke basu gwale-gwale sannan suka yi barazanar garkuwa da Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamnan Jihar Kaduna da wasu ‘yan majalisa in har basu biya musu bukatunsu ba.

Yayin mayar da martani akan bidiyon, Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya ce:

“Yan ta’adda suna amfani da farfaganda tare da son amfani da karfi don gwamnati ta amince ko ta mika wuya ga bukatunsu, kuma hakan ba sabon abu bane.”

Yayin mayar da martani ga maganar Shehu, Malam Bello Yabo ya nuna rashin jindadinsa akan yadda kakakin ya kira bidiyon da farfaganda.

Ya zarge shi da rashin nuna damuwa akan wadanda aka yi garkuwa dasu kuma ya yi fatan Shehu ya fada hannun ‘yan bindigan.

“Ina addu’ar ayi garkuwa da kai, Garba Shehu kuma a kwatanta hakan da farfaganda,” inji Yabo.

Ya bukaci ‘yan bindigan da su saki wadanda suka kama wadanda basu ji ba basu gani ba, ya kuma yi fatan ‘yan ta’addan su samu nasarar yin garkuwa da wadanda suka yi barazanar kamawa.

“Muna muku addu’a masu garkuwa da mutane. Ubangiji ya baku nasarar yin garkuwa da wadanda ku ka yi barazanar yin garkuwa dasu. Amma ku taimaka ku saki wadanda ku ka kama.

“Idan har irin mutanen da ku ke garkuwa dasu kenan, ba za mu taba damuwa ba. Sai dai muyi muku addu’o’i don sun zame mana bala’i.

“Wadannan mutanen babu irin alkawuran da basu yi mana ba, amma yanzu sun samu dama akan mu. Ku sace su, ku kai su daji kuma ku zane su, maimakon cin zarafin wadanda basu ji ba basu gani ba.

“Ku taimaka ku yi abubuwan da ku ka yi barazanar yi, mu kuma za mu taya ku da addu’o’i,” a cewar Malamin.

A baya, malamin dan gani kashenin shugaban kasa ne, amma yanzu ya dawo daga rakiyarsa.

Yau za a gurfanar da Amira Sufyan, budurwar da tayi karyar an yi garkuwa da ita gaban kotu

Ana sa ran rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Abuja za su gurfanar da Amira Safiyan, gaban kotun majistare da ke Wuse a yau ranar 29 ga watan Yunin 2022 bisan yin karyar ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ita.

A ranar 14 ga watan Yuni ne Amira ta bayyana a Twitter inda ta ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ita da wasu mutane 16 ciki har da mata 3 masu juna biyu, LIB ta ruwaito.

Nan da nan mutane su ka razana bayan ta ce wadanda su ka yi garkuwa da su su na sanye da kayan ‘yan sanda ne sannan har gida su ka je su ja dauke su.

Bayan an gano inda take, ta bayyana a kafar taba bada hakuri inda tace da kanta ta je daji ta ki cin komai bisa ganganci.

Kamar yadda ta wallafa:

“Don Allah duk mai lambata ta WhatsApp ya duba don na tura sakon inda nake. Bayan wasu masu garkuwa da mutane sanye da kayan ‘yan sanda sun zo har gida sun sace mu a bangarori daban-daban a Abuja. Mu 17 ne kuma a ciki akwai mata 3 masu juna biyu da kananun yara guda 2.”

‘Yan sanda za su tuhumi Amira akan yada labarin karya don rikita mutane a yau.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe