32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Iyayen budurwa sun fatattake ta bayan ta haifa musu jaririn balarabe daga dawowa Saudiyya yin aikatau

LabaraiIyayen budurwa sun fatattake ta bayan ta haifa musu jaririn balarabe daga dawowa Saudiyya yin aikatau

Jama’a sun tallafawa wata budurwa wacce iyayenta suka fatattaketa bayan ta haifa musu jaririn balarabe bayan ta dawo daga Saudiyya, Legit.ng ta ruwaito.

Kamar yadda wata Judy Oricho mai tallafawa masu kananun karfi ta bayyana a shafinta na Facebook, wanda Anna Awuor mai shekaru 29 ta fuskanci cin zarafi ne daga wanda take aiki karkashinsa, daga nan ta samu ciki.

“Bayan fahimtar ta kusa haihuwa ne aka mayar da ita Kenya. Daga bisani ta haihu wanda hakan yayi sanadiyyar da aka fatattake ta da jaririn balaraben da ta haifia,” inji Oricho.

Ganin hakan ne yasa ta nufi Migori tana neman tallafin wata ‘yar uwarta, ashe itama ta tashi. Hakan yasa ta nufi sansanin Migori don neman taimako.

“Tana neman ko wanne irin taimako, abinci, suttura da kuma wurin kwana tare da jaririnta,” a cewar Oricho.

Ta yi nasarar samun taimakon don mazauna Kenya da dama dun tausaya mata wanda hakan yasa wata kungiya ta tallafa mata.

“Nagode sosai, kuma ina farincikin sanar da ku cewa an kai kuka akan lamarin ga kungiyar Harvest Hope of Africa wadanda suka amshe ta da yaron nata,” inji Oricho.

Mata daya ta isheka rayuwar duniya, Cewar babban malamin Saudiyya mai mata 2

Dr Aa’ed Al-Qarni ya ce mace daya ta ishi namiji a wani shiri na Trend KSA na MBC Talk Show, LifeinSaudiArabia.net ta ruwaito.

Kamar yadda ya bayyana, AlQur’an ma ya bukaci mutum ya auri mace daya idan har ya tabbatar a zai iya adalci ba tsakanin matanka, kuma ya ja kunne kwarai akan gazawar nan wacce mutane ba su damu da tunawa da ita ba.

A bayyana yake cewa musulunci bai amince mutum ya kara aure don nishadi ba, sai don taimako ga zawarawa da marayu yayin da rayuwarsu take cikin matsanancin yanayi.

“Ana karin aure ne don taimakon jama’a saboda hakan addinin musulunci ya koyar a ko wanne mataki na rayuwarmu,” inji malamin.

Ya ci gaba da cewa:

“Idan ka san zaka iya kulawa da bazawara ko kuma marainiya kadai, za ka iya aurenta ta kasance matsayin matarka amma kada a manta da dokar ta farko wacce tace wajibi ne adalci tsakanin mata.”

Sai dai shi kanshi Dr. Aa’eed Al-Qarni matansa biyu

Bayan wadannan kalaman sun fito daga bakinsa mutane sun dinga mamaki kasancewar matansa biyu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe