24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yadda Giwa ta halaka wata mata kuma ta bi gawarta ta tattake ana tsaka da jana’iza

LabaraiYadda Giwa ta halaka wata mata kuma ta bi gawarta ta tattake ana tsaka da jana’iza

Wata giwa ta halaka wata tsohuwa mai shekaru 70 sannan ta bi inda ake jana’izar matar ta tattake gawarta, Aminiya ta ruwaito.

Saidai tana kammala aika-aikar ta tsere daga wurin bayan ta halaka matar a lokacin da mutane da dama suka taru su na kallon ikon Allah kamar yadda ‘yan sanda su ka bayyana.

Lamarin ya auku ne ga matar mai suna Maya Murmu a kauyen Raipal da ke gabashin kasar Indiya.

Har ila yau, ana tsaka da jana’izar matar da yamma, giwar ta kara komawa inda ta tattake gawarta kamar yadda jaridar Press Trust da ke Indiya ta bayyana.

Kamar yadda labarai su ka nuna, bayan yin aika-aikar, giwar ta tsere daga gidan namun daji da ke Dalma a garin Maturbhanj mai nisan kimanin kilomita 200.

Ba wannan bane karon da giwar ta fara halaka jama’a, a watan Oktoban da ya gabata, ta halaka wani tsoho nai yawon bude ido a gaban idon dansa a Zimbabwe.

Sannan ta taba halaka shugaban mafarauta na yankin Victoria Falls da ke yammacin Zimbabewa mai shekaru 35 da haihuwa.

Akwai mutane da dama da su ke zargin tsohuwar da yin yunkurin farautar giwar wanda hakan ya sanya ta halakata.

An aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mata 3 a Iran bisa halaka mazajen su

Wata amarya mai ƙananan shekaru ƴar ƙasar Iran wacce ta halaka mijin da aka tilasta mata aure tana da shekara 15 a duniya, na daga cikin mata uku waɗanda aka aiwatarwa da hukuncin kisa bisa halaka mazajen su a cikin wannan satin.

Soheila Abadi, mai shekara 25 yanzu, an rataye ta a gidan kurkuru bayan an yanke mata hukunci bisa halaka mijinta akan ‘saɓanin iyali’ a cewar bayanan kotu. Shafin LIB ya rahoto.

An kuma aiwatarwa da wasu mata biyun  hukuncin kisa a ranar Laraba bisa laifin halaka mazajen su.

Kotuna ba suyi wa matan da suka halaka mazajen su adalci a ƙasar

Masu rajin kare haƙƙin bil’adama sun yi iƙirarin cewa kusan duk lokacin da mata suka halaka mazajen su, to ana cin zarafin su ne a gida amma kotunan ƙasar Iran basa la’akari da hakan.

Matan guda uku na daga cikin mutane 32 da aka rataye a ƙasar a cikin satin da ya gabata.

Ana yawan aiwatar da hukuncin kisa a Iran

Hakan na zuwa a yayin da ake daɗa samun ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar, inda aƙalla mutum 251 aka kashe a farkon watanni 6 na wannan shekarar. A cewar rahoton Amnesty International.

Yawan mutanen ya ninka adadin da aka kashe a shekarar da ta gabata a irin wannan lokacin.

Daga cikin mutum 251 da aka halaka, 146 daga ciki masu laifin kisan kai ne, sannan aƙalla 86 masu laifuffukan ƙwayoyi ne wanda bai cancanci hukuncin kisa ba a dokar ƙasa da ƙasa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe