27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Hotuna: Yadda ‘ya’yan marigayi Yar’adua su ka dauki wankan kece raini a liyafar auren dan’uwansu

LabaraiHotuna: Yadda ‘ya’yan marigayi Yar’adua su ka dauki wankan kece raini a liyafar auren dan’uwansu

Idan ba a manta ba, tun a makon da ya gabata aka daura auren Shehu Umaru Musa Yar’adua, wanda da ne ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar’adua da kuma Yacine Sheriff.

Bikin nasu ya yi matukar daukar hankali kasancewar su biyu ‘ya’yan manyan mutane ne kuma hamshakan masu kudi da masu mulki har da uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari sun halarci daurin auren.

Gwamnoni, ministoci, sanatoci, manyan ‘yan kasuwa da sauran manyan mutane sun isa daurin auren a jiragen saman su fiye da goma wanda hakan ya karkatar da hankalin ‘yan Najeriya.

A wannan makon ma ba a tsaya daga bukukuwan ba, don shagulgula iri-iri kamar bridal shower, wushe-wushe da sauransu da aka dinga yi ana barin nairori.

Yayyin ango, kanni da ‘ya’yan ‘yan uwansa babu shakka sun dauki hankalin jama’a musamman idan aka kalli irin kayan alfarmar da suka sanya zuwa liyafar auren.

Sun sanya tsadaddun sarkoki da ‘yan kunnaye tare da samun masu kwalliyar da ake ji dasu don su fitar dasu kunya kuma tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ga wasu daga hotunan kamar yadda shafukan theweddingstreet_ng da arewafamilyweddings na instagram suka nuna ‘yan uwan nasa wadanda cikinsu akwai matar tsohon gwamnan Jihar Kebbi, Dakin Gari, tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema da sauransu.

Da sauran karfinsa: Bidiyon Obasanjo yana girgijewa tare da diyarsa a liyafar aurenta

Wani bidiyo ya bayyana a shafin Arewa Family Weddings da ke Instagram wanda aka ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo yana kwasar rawa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, ya rike hannun diyarsa ne wacce take sanye da kaya masu kala bula yayin da yake sanye da farar babbar riga.

Mutane da dama sun yi mamakin yadda duk da tsufarsa ya zage damtse wurin ganin bai bayar da kunya ba.

Lamarin ya bai wa mutane da dama mamaki musamman idan aka kalli tsufarsa da yadda yake fama da ciwon suga.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe