
An kama wasu mutane hudu da ake zargi da sakin bayanai ga ‘yan ta’adda game da wuraren da sojojin Najeriya ke hidima da kuma zirga-zirga a wajen Abuja.
Wani jami’in leken asirin da ya bayyana kamun ga Jaridar PR Nigeria, ya ce tuni masu laifin suna hannun wata hukumar tsaro a Abuja.
A cewar jami’in ‘yan sandan, an kama wadanda ake zargin ne da nagartattun kayan aiki da suka hada da na’urar wayar,revolver, wukake, da layu, da kuma tsofaffin wayoyi na kasar Sin, wadanda ba sa amfani da data.
Majiyar wadda ta kasance cikin tawagar da su ka kai samamen ga masu fitar da bayanan, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi don sanin masu daukan nauyin su.
Majiyar ta kara da cewa ayyukan masu kai bayanai ga ‘yan ta’adda sun hada da hare-haren da aka kai baya-baya nan a, babban birnin tarayya, FCT.
A halin yanzu dai ana ci gaba da yiwa wadanda ake zargin tambayoyi domin tantance ko suna aiki da kungiyoyin ta’addanci ko ‘yan fashi da makami ko kuma wasu da ke da wata manufa.
“Zan iya sanar da ku cewa, da gangan sojoji suka ki bayar da bayanai tun bayan harin da aka kai gidan yarin Kuje, har zuwa harin da aka kai wa sojoji a titin Bwari da Zuma Rock, ya zuwa yanzu rundunar tsaron hadin gwiwa ta kashe sama da mutane 70 dauke da makamai. majiyar ta kara da cewa, wadanda suka hada da ‘yan gidan yarin Kuje da suka gudu da kuma ‘yan ta’adda.
Buhari bai san da barazanar ƴan ta’adda na sace shi ba har sai da na gaya masa -El-Rufai
A wani labarin kuma Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana cewa shine wanda ya sanar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari batun barazanar ƴan ta’adda ta sace shi. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
A wani bidiyo da aka saki a ƙarshen mako, ƴan ta’addan waɗanda suka sace fasinjojin jirgin ƙasa a watan Maris, sun yi barazanar sace shugaba Buhari da El-Rufai.
Da yake magana a wani shiri a gidan rediyo wanda wakilin jaridar ya bibiya a daren ranar Laraba, gwamnan yace shi kan shi an gargaɗe shi kan tsoma iyalan gidan sa.
El-Rufai ya daɗe yana kira da ayi ruwan bama-bamai kan ƴan ta’adda
Ya kuma ƙara bayanin cewa a shekaru biyar da suka gabata yasha yin kira kan ayi ruwan bama-bamai kan sansanin ƴan ta’adda a duk inda suke, yana mai cewa hakan shine kaɗai maganin matsalar.
Naji labarin wani bidiyo inda suka yi barazanar sace Buhari da ni kaina. An gargaɗe ni na kula wurin sanya iyalai na. Ta ya zamu kasance a ƙasa da sojoji, ƴan sanda da gwamnatin tarayya amma wasu ƴan ta’adda na barazanar sace shugaban ƙasa?
Shugaba Buhari ya bayar da umurnin a murƙushe ƴan ta’adda
Shugaban ƙasa ya tabbatar min cewa ya gana da hafsoshin tsaro kwana 3 zuwa 4 kafin haɗuwar mu sannan ya basu umurnin cewa su murƙushe waɗannan mutanen da ƙarfin soji. Muna fata Insha Allah cewa sojoji da ƴan sandan da aka ba wannan umurnin za su gaggauta kammala aikin. Ba sai mun jira har sai ƴan ta’adda sun kawo hari kafin mu mayar da martani ba.
Dole sojoji su bi su duk inda suke suyi maganin su. Maganar gaskiya itace mun damu kan matsalar tsaro amma muna fatan gwamnatin tarayya za tayi abinda