27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Masha Allah: Fatima Payman, musulma mai Hijabi ta farko da aka zaba a matsayin Sanata a kasar Australia

LabaraiMasha Allah: Fatima Payman, musulma mai Hijabi ta farko da aka zaba a matsayin Sanata a kasar Australia

Mace ta farko da ke sanya Hijabi ta ja hankalin jama’a bayan ganin ta lashe zabe a matsayin ‘yar majalisar dattawa a yammacin Australia ranar 20 ga watan Yuni, wanda hakan yasa ta kafa tarihin zama sanata ta farko mai sanya Hijabi a gabadaya tarihin kasar Australia kuma sanata mai mafi karancin shekaru, Theislamicinformation.com ta ruwaito.

Sunanta Fatima Payman, shekarunta 27 kuma asali ‘yar gudun hijira ce wacce ta baro Afghanistan zuwa Australia lokacin tana da shekaru 8 da haihuwa.

A jawabinta na farko a mukamin, cike da hawaye Payman ta bayyana farincikinta akan yadda mahaifinta yayi sadaukarwa mai yawa akanta, wanda ya zauna a Australia a matsayin dan gudun hijirar Afghanistan kuma ya rasu a 2018.

Cike da alfahari Payman tace wa yayi zaton matashiya mai karancin shekaru da aka haifa a Afghanistan kuma diyar dan gudun hijira zata taba zama ‘yar majalisa a Australia.

Payman ta ci gaba da bayyana yadda mahaifinta ya sadaukar da kansa wurin gina rayuwarta. Ta bayyana yadda yayi kananun ayyuka kamar direban tasi, mai gadi da sauransu duk don tara kudin da zai kula da ita da kanninta uku.

Sai dai a cewarta duk da dagewar mahaifinta don ganin sun samu rayuwa mai inganci shi bai dage akan kansa ba.

Payman wacce shekarunt 8 lokacin da ita, mahaifiyarta da kanninta uku suka koma Australia da zama a shekarar 2003 inda suka biyo mahaifinta wanda ya isa kasar a 1999.

A cewarta, ganin dagewar iyayenta ne ta zage damtse inda ta yi karatu a kwalejin musulunci ta Australia har ta zama likita.

Ganin tana son siyasa ne yasa ta shiga Kungiyar Hadin Kan Ma’aikata, kungiyar kwadago mafi girma a Kasar Kangaroo. Daga bisani aka zabeta a matsayi sanata a Jam’iyyar Kwadago ta Australia.

Zaben Payman da aka yi ne yasa ta zama mace ta farko sannan sanata mai karancin shekaru ta uku da ke sanya Hijabi a tarihin Australia, inda yanzu haka shekarunta 27 da haihuwa. Yanzu kuma ita ce sanata mafi karancin shekaru a majalisar dattawan kasar.

Sai abin ban tausayi shine yadda mahaifinta ya rasu sakamakon fama da cutar kansar jini a 2018. Mahaifinta bai samu damar ganin diyarsa ta zama sanata ba.

Dangane da ra’ayinta na amfani da Hijabi, Payman ta ce ya kamata wadanda suke zato akanta saboda shigarta su fahimci cewa zabinta ne sanya hijabi.

Ta shawarci yara mata da suke son amfani da hijabi da su yi alfahari da msgi sannan su dage wurin neman ilimi don suna da damar yin hakan.

Da ɗumi-ɗumi: Kotun ƙoli ta amince ɗalibai musulmai sanya hijabi a makarantun jihar Legas

Kotun ƙoli ta tabbatar da ‘yancin da ɗalibai mata su ke da shi a jihar Legas na sanya hijabi ba tare da nuna mu su wariya da tsangwama. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

An tabbatar da hukuncin damar sanya hijabi a makarantun jihar Legas

Kotun ƙolin ta tabbatar da wannan hukuncin ne yau Juma’a a birnin tarayya Abuja.

Alƙalan da su ka saurari ƙarar dai sun haɗa da, mai shari’a Olukayode Ariwoola, Justice Kudirat Kekere-Ekun, mai shari’a John Inyang Okoro, mai shari’a Uwani Aji, mai shari’a Mohammed Garba, mai shari’a Tijjani Abubakar, da mai shari’a Emmanuel Agim.

Biyar daga cikin alƙalan sun amince da ɗaliban su yi amfani da hijabi, yayin da biyu daga cikin su ba su aminta ba.

Yadda taƙaddamar sanya hijabi ta faru a jihar

Wata babbar Kotun jihar Legas, a 17 ga watan Oktoban 2014, ta haramta yin amfani da hijabi a makarantun jihar, hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara tayi watsi da shi a 21 ga watan Yuli, 2016.

Kotun ɗaukaka karar ta yi nuni da cewa, dokar hana sanya hijabin wata tsangwama ce ga ɗalibai musulmai na jihar Legas.

Rashin gamsuwa da hukuncin ya sanya gwamnatin jihar Legas, garzaya wa zuwa kotun ƙoli.
 
Gwamnatin jihar Legas dai ta sanya dokar hana ɗalibai musulmai sanya hijabi a makarantun gwamnati na jihar, a watan Agusta, 2018.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe