31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Muhimman abubuwan sani game da rigar ɗakin Kaaba (Kiswa)

IlimiMuhimman abubuwan sani game da rigar ɗakin Kaaba (Kiswa)

Kiswa itace baƙar rigar da ake lulluɓe ɗakin Kaaba da ita. Sannan tana zuwa da wasu muhimman abubuwa da yakamata ace an san da su.

Ranar da ake sauya Kiswa rigar ɗakin Kaaba

A ranar 9 ga watan Dhul Hijjah, ana sauya Kiswa, wannan daɗaɗɗiyar al’ada ce wacce aka shafe shekaru ana gudanarwa. Annabi Isma’il (AS) ya fara kimanin shekaru 4000 da suka wuce kafin annabi Muhammad (SAW) ya fara da’awar musulunci.

Jaridar The Islamic Information ta tattaro wasu muhimman abubuwa da yakamata ku sani.

1. Sauya rigar Kiswa da bayar da kyautar ta

A kowace shekara idan aka sauya rigar Kiswa, ana yayyanka ta domin bada kyautar ta ga wasu zaɓaɓɓun mutane domin karramawa. Wasu kuma suna rabawa Alhazan da suka zo aikin Hajji daga faɗin duniya.

2. Adadin kuɗin yin sabuwa yana kai SAR 17m

Rigar Kiswa tana da yadi 47 sannan tana da tsawon 658 sq. m da kuma nauyin kilogram 670. Sannan tana ɗauke da kilogram 15 na zallar zinare.

3. Ana sauya launin Kiswa

An sha sauya launin rigar ɗakin Ka’aba a zamanin Khalifofi da sarakuna. A lokacin annabi Muhammad (SAW), ta kasance launi fara, yayin da a wasu ƙarnukan launin ja da shuɗi, sannan daga ƙarshe yanzu ana amfani da launin baƙi.

4. Mutumin da ya sauya Kiswa

Asad Al Himairi, mutumin ƙasar Yemen, shine mutum na farko da ya fara lulluɓe Kaaba. A zamanin baya, ƙabilu daban-daban zasu haɗu su lulluɓe Kaaba.
Shugabannin ƙabilun kuma za su kawo labulaye domin lulluɓe bangon Kaaba.

5. Ƙasashen Yemen, Egypt, da Iraq ke samar da yadin Kiswa

Gabaɗaya yadin dake a jikin rigar Kiswa yana zuwa ne daga Baghdad, Iraq, Yemen da Egypt. Mohd Ali Pasha, gwamnan Egypt shine ya ƙirƙiro hanyar yin wannan rigar, sannan ya mayar da alhakin yin ta a ƙasar bayan sun rabu da daular Turkiyya.

6. An canja ranar sauya rigar Kiswa

A da can da farko, ana sauya rogar Kiswa a ranar 10 ga watan Dhul Hijjah amma an sauya zuwa ranar 9 ga watan Dhul Hijjah. Sai dai a wannan shekarar ta bana an sauya rigar Kiswa a ranar 1 ga watan Muharram 1444.

Yadda aka sauya rigar ɗakin Ka’aba da sabuwa mai darajar N2.7bn

A wani labarin kuma mun kawo muku yadda aka sauya rigar ɗakin Kaaba da sabuwa mai darajar kuɗi N2.7bn.

Ɗakin Kaaba ya samu sabuwar riga wato Kiswah, bayan da aka sauya waccan ta da, an dai kashe dala miliyan 6.5 (N2.7bn) wajen ɗinka sabuwar rigar wacce aka saka ta a safiyar wannan Asabar ɗin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe