31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Mata daya ta isheka rayuwar duniya, Cewar babban malamin Saudiyya mai mata 2

LabaraiMata daya ta isheka rayuwar duniya, Cewar babban malamin Saudiyya mai mata 2

Dr Aa’ed Al-Qarni ya ce mace daya ta ishi namiji a wani shiri na Trend KSA na MBC Talk Show, LifeinSaudiArabia.net ta ruwaito.

Kamar yadda ya bayyana, AlQur’an ma ya bukaci mutum ya auri mace daya idan har ya tabbatar a zai iya adalci ba tsakanin matanka, kuma ya ja kunne kwarai akan gazawar nan wacce mutane ba su damu da tunawa da ita ba.

A bayyana yake cewa musulunci bai amince mutum ya kara aure don nishadi ba, sai don taimako ga zawarawa da marayu yayin da rayuwarsu take cikin matsanancin yanayi.

“Ana karin aure ne don taimakon jama’a saboda hakan addinin musulunci ya koyar a ko wanne mataki na rayuwarmu,” inji malamin.

Ya ci gaba da cewa:

“Idan ka san zaka iya kulawa da bazawara ko kuma marainiya kadai, za ka iya aurenta ta kasance matsayin matarka amma kada a manta da dokar ta farko wacce tace wajibi ne adalci tsakanin mata.”

Sai dai shi kanshi Dr. Aa’eed Al-Qarni matansa biyu

Bayan wadannan kalaman sun fito daga bakinsa mutane sun dinga mamaki kasancewar matansa biyu.

Amma mahangar Al-Qarni itace mutum ya tabbatar ya kiyaye aure-aure har sai yana da kwakkwarar hujjar yin hakan.

Majalisar dinkin duniya ta daura dammarar hana maza auren mace fiye da daya

Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar yaki da cin zarafin mata sun bukaci haramta auren mace fiye da daya saboda abunda da suka kira kare ‘yancin mata a duniyarfi.fr ta ruwaito.

Alkaluman hukuma sun bayyana cewa kashi 2 ne kadai na fadin duniya ke zama a gidajen da ke da mata fiye da daya, sakamakon binciken Cibiyar Pew dake Amurka , wanda ta gudanar a kasashe 130 da kuma wasu yankuna.

Rahoto ya bayyana akan haramta auran mace fiye da daya a kasashen duniya da dama, wanda ya hada da nahiyar Turai, sai dai kuma matakin ya halasta a kasashen Gabas ta Tsakiya da Asia da kuma wasu yankunan Afirka.

Sakamakon binciken da ya gudana ya bayyana yadda aka fi samun auren mata da dama a yankin Afirka ta kudu da sahara, yayin da kashi 11 na al’ummar yankin suka fita daga gidajen da ake auren mata da dama.

Banciken ya nuna yadda kashi 37 na Burkina Faso na auren mata sama da daya, inda kashi 34 suka fito daga Mali, kashi 30 a Gambia sannan kashi 29 daga Jamhuriyar Nijar.

Alamu sun nuna yadda kashi 28 na ‘yan Najeriya ke da mata sama da daya, yayin da Guinea ke da kashi 26.

Sakamakon binciken ya tabbatar da yadda aka fi samun auran mace sama da daya a tsakanin al’ummar Musulman Afirka, wanda ya sha bamban da na Kiristoci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe