23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Tinubu zai mayar da Najeriya babbar cibiyar tattalin arziƙi ta duniya -shugaban matan APC

LabaraiTinubu zai mayar da Najeriya babbar cibiyar tattalin arziƙi ta duniya -shugaban matan APC

Shugaban matan jam’iyyar All Progreasive Congress (APC) ta ƙasa, Betta Edu, tayi kurin cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai iya mayar da Najeriya cibiyar tattalin arziƙi ta duniya.

Channels Tv ta rahoto cewa tayi wannan furucin ne a wurin wani taro da matasan matan jam’iyyar a Abuja, inda ta roƙi dukkanin matan jam’iyyar da su fara neman magoya baya ga ɗan taƙarar shugaban ƙasa na jami’yyar a zaɓen 2023, Tinubu.

images 12
Shugaban matan jam’iyyar APC ta ƙasa, Betta Edu.

Tinubu yafi sauran ƴan takara cancanta

A cewar Edu, Tinubu shine ɗan takarar da yafi cancanta a 2023 wanda zai gyara Najeriya.

Shugaban matan kuma ta buƙaci taron matan da su fara bi gida-gida suna yaƙin neman zaɓe.

Zama a cikin gida kuna cewa ku taron matasan mata ne ba zai haifar da komai ba.

Lokaci yayi da yakamata mu farka. Lokaci yayi na barin wasa da gulmace-gulmace. Lokaci yayi na zuwa tituna, gida-gida, inuwa-inuwa, shago-shago, daga wannan matashiyar zuwa kan wata, daga wannan shafin a Twitter zuwa wani, daga wannan shafin a Facebook zuwa wani, daga wannan shafin a Instagram zuwa wani.

Saboda muna da tabbacin cewa idan har Tinubu zai iya gyara Legas, wacce tafi wasu ƙasashen yawa, mai mutane sama da miliyan 20, ya mayar da ita zuwa cibiyar tattalin arziƙin Najeriya, lallai zai iya mayar da Najeriya cibiyar tattalin arziƙi ta duniya.

Lokaci yayi da zamu fara wannan tafiyar. Kada surutan da ku ke gani a kafafen sada zumunta su ɗauke muku hankali. A maimakon hakan ku mayar da hankali kan manufar da kuke son cimmawa.

Ganduje ya bayyana muhimmin dalilin da yasa Tinubu ya ɗauki musulmi a matsayin mataimaki

A wani labarin na daban kuma, Ganduje ya bayyana dalilin zaɓar musulmi a matsayin mataimaki da Tinubu yayi.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yace ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓi musulmi ne a matsayin abokin takarar sa domin kawar da muhimmanci na musamman da ake ba addini a siyasar Najeriya

Ganduje wanda yana a gaba-gaba cikin masu yaƙin neman zaɓen Tinubu, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake magana da ƴan jarida a masallacin Juma’a na Unguwar Sabo, a Osogbo, babban birnin jihar Osun. Jaridar

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe