31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda aka sauya rigar ɗakin Ka’aba da sabuwa mai darajar N2.7bn

LabaraiYadda aka sauya rigar ɗakin Ka'aba da sabuwa mai darajar N2.7bn

Ɗakin Kaaba ya samu sabuwar riga wato Kiswah, bayan da aka sauya waccan ta da, an dai kashe dala miliyan 6.5 (N2.7bn) wajen ɗinka sabuwar rigar wacce aka saka ta a safiyar wannan Asabar ɗin.

BBC Hausa ta rahoto cewa an fara aikin sauya rigar tun cikin daren Juma’a bayan Sallar Isha’i zuwa asubahin ranar Asabar, wanda ya zo daidai da ranar 1 ga watan Muharram na shekarar 1444 A.H.

Sabuwar rigar Ka’aba na da nauyi matuƙa

An kiyasata cewa sabuwar rigar nauyinta ya kai kilogram 850, kuma a yanzu ta kasance riga mafi tsada irin ta a duniya.

Ka'aba
Yadda aka sauya rigar ɗakin Ka’aba da sabuwa mai darajar N2.7bn Hoto daga Haramain Sharifain.

Wannan dai shi ne karon farko da ake sauya rigar ɗakin Ka’aba (Kiswah)wato kamar yada ake kiran rigar, a ranar 1 ga watan Muharram.

Kafin wannan lokaci ana sauya rigar ɗakin Kaaba ne a lokacin da ake gudanar da aikin Hajji, musamman a safiyar 9 ga watan Dhul Hijjah idan alhazai sun tafi hawan Arafa.

An bayyana dalilin canja lokacin sanya sabuwar rigar

A ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais da ke kula da manyan masallatan biyu mafiya daraja a duniya, ya ce an sauya lokacin sauya rigar Kaaba ne bisa sabbin dokoki da shawarwari masarautar Saudiyya.

Mutane sama da 200 ne dai kafofin yada labarai suka rahoto cewa ne suka yi aiki akan rigar Kaaba, tun daga wajen ɗinkata har zuwa sanyata a jikin ɗakin Kaaba.

Mai rubutun adon Kiswa na Ka’aba Rajab Mahoos ya rasu bayan hidima ta shekara 47

A wani labarin kuma Rajab Mahoos mai rubutun adon Kiswa ya rasu bayan shekaru 47 yana hidima.

Dan asalin kasar Saudi Arabia mai suna Rajab Mahoos Al maliki, daya daga cikin manyan masu yin kwalliyar zinare na dakin ka’aba, ya rasu bayan ya shafe shekara 47 yana hidimar dakin Ka’aba. 

A Saudi Arabia akwai wani birnin na musamman da aka ware domin yin ado ga dakin ka’aba  wanda aka fi sani da Kiswa.

Mamacin ba kawai rayuwar sa ya bayar ga hidimar Kiswa ga dakin Ka’abar ba, a’a aikinsa yana yinsa cikin karsashi da nishadi da kuma salo. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe