Wani mutum wanda ba a san ko waye ba ya rasa ransa bayan an kawo wutar lantarki a Isale-Agbede a cikin yankin tsibirin jihar Legas.
Ya rasu yana tsaka da satar keburan lantarki
Jaridar The Punch ta tattaro cewa mutumin ya rasu ne yayin da yake satar kebur a jikin wata transifoma (gidan wuta) a yankin.
A bidiyon da wakilin jaridar ya gani ranar Asabar, ya nuna gawar mutumin maƙale a tsakanin transifomomi guda biyu yayin da kuma ga wasu manyan kebura guda uku a wurin da lamarin ya auku.
Lamarin ya auku ne kwanaki kaɗan bayan an sauya keburan bayan wasu zauna gari banza sun sace waɗancan.
Wani mai amfani da kafar Twitter mai amfani da sunan Teewhy wanda ya saka bidiyon ya rubuta cewa mutane sun ɗauka cewa mutumin ma’aikacin hukumar rarraba wutar lantarki ta Eko Electric Distribution Company ne.
Yace:
Wannan mutumin yayi ƙoƙarin sace kebura daga jikin transifoma amma cikin tsautsayi aka dawo da wutar NEPA, nan take ya mutu. Ya faru ne a wani wuri cikin tsibirin jihar Legas. Mutane da yawa sun ɗauka ma’aikatan NEPA ne ke zuwa suna sace keburan.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin hukumar rarraba wutar lantarki ta EKEDC, Mr Felix Ofulue, sun ci tura inda wayar salular ta kasance a rufe har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Da aka tuntubi kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace har yanzu ba a gano kowaye mutumin ba.
Hundeyin yace:
Mun samu labarin aukuwar lamarin amma mutumin har yanzu ba a gano kowaye ba. Ana cigaba da gudanar da bincike.
Yan sanda sun kama wani matashin barawo da ya kware wajen satar akwatinan talabijin a otal-otal
A wani labarin kuma ƴan sanda sun yi ram da ɓarawon akwatinan talabijin a otal-otal.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Ido, sun damke wani barawo mai suna Ahmed Ibrahim, wanda ya kware wajen satar talabijin ta bango a Otal a jihar.
An tabbatar da cewa, barawon yana kama daki ne a hotal din, kuma idan ya gama zaman sa sai ya sace talabijin daga dakin ya tafi da ita.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com