23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Sai matata ta amshi kudade masu kauri sannan take yarda mu yi kwanciyar aure, Magidanci gaban kotu

LabaraiSai matata ta amshi kudade masu kauri sannan take yarda mu yi kwanciyar aure, Magidanci gaban kotu

Adegbenga Dada, wanda injiniyan ruwa ne kuma dan wani basarake daga Eruku a karamar hukumar Ekiti cikin Jihar Kwara ya koka akan yadda matarsa take amshe masa kudadensa kafin ta amince dashi a shimfidar aurensu, LIB ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a wata takardar kara wacce ya gabatarwa babbar kotun Kwara da ke zama a Ilorin.

Dada ya nemi a warware aurensu mai shekaru 28 da Roseline Dada akan zarginta da neman maza.

Ya zargi matarsa da kin sanin darajar kanta inda ya kara da cewa hakan ya kawo cikas ga zamantakewarsu sannan tana tura ‘yan matan wurin maza daban-daban don su amso mata kudi.

Adegbenga, wanda asalin dan Kwara ne amma mazaunin Legas ya ci gaba da cewa:

“Matata bata amsa tayin shimfidar aurena don ta koma dakin baki. Sai ta amshi kudade mai kauri sannan take amincewa ta bayar da kanta gareni. Idan har ban bata kudin ba ba za ta yarda da ni ba.

“Aurena ya lalace saboda ni da matata ba ma zama don tattaunawa akan rayuwarmu da ta yaranmu.”

Ya nemi kotu ta ba shi damar rike yaransa 3 da suka haifa.

A bangaren Roseline, ta musanta duk zargin da mijinta yayi mata inda tace shi ne manemin matan.

Ta ci gaba da cewa babu komai don an raba aurensu, amma kotu ta taimaka ta ba ta damar mallakar ginin hadakar da suka yi tare a Legas ita da mijinta.

A bangaren mijin, ta lauyansa, Josiah Adebayo ya ce akwai hotunan tsiraicinta da ya samu a wayarta wanda ta turawa saurayinta, kuma ba don tozarta ta gabatar da shi ba, sai don tabbatar da gaskiya maganarsa.

Alkalin kotun, Justice S.T Abdulqadri ta amince da batun raba aure inda tace ta yarda da duk hujjojin lalatar da aka gabatar gabanta.

Ta tsaya akan cewa Dada bata da kaso a gidansu na Jihar Legas.

Sannan kotun bata bai wa ko wanne daga cikinsu damar rike yaran da aurensu na shekaru 28 ya samar ba, inda tace duk yaran sun wuce shekaru 20 don haka sun san ciwon kansu.

Wata mata ta maka mijin ta a kotu saboda ya auro aminiyar ta a matsayin kishiya a gareta 

Wata mata matashiya ‘yar shekara 25 mai suna Firdausi Musa, ta maka tsohon mijin ta mai suna Saidu Abubakar a kotu, a garin Kaduna, saboda ya auro mata aminiyar kawar ta a matsayin kishiya. 

Da take bayani, lauyar mai karar, mai suna Zainab Murtala, ta ce, mijin matar ya kwashe kayan ta dake cikin akwati da sauran kyaututtukan da ya bata, duk ya mallakawa sabuwar amaryar ta sa. 

Auren matar bai dade ba

A cewar ta,

” Kwananan muka yi aure da shi, amma bamu tare a kowanne gida ba, tsawon wata biyu ke nan, kawai dai ya kama hotal ne, a can ne muke haduwa “. 

“Kwatsam sai ya ce, ya sake ni, daga baya ya mayar dani muka ci gaba da zama, sai ya sake saki na, inda daga nan sai ya auro kawata aminiya ta, kuma ya mallaka mata duk kayayyaki na, wanda ya hada har da dukkan kayan sawa ta”.

Ta fada 

Ta nemi kotu da ta dawo mata da kayan ta

Ta roki kotu da ta dawo mata da kayan ta, da aka kwashe mata, har ma da wadanda ta sanya kudin ta, ta siya yayin da taje Umarah a kasa mai tsarki. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe