37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Kabilar Hamar: Maza na gane juriyar mata ta hanyar zuga musu bulalai yayin da matan Ke kwasar rawa ana kidi

LabaraiKabilar Hamar: Maza na gane juriyar mata ta hanyar zuga musu bulalai yayin da matan Ke kwasar rawa ana kidi

Matan kabilar Hamar da ke Ethopia suna yin wani biki mai suna “Maza”, wanda maza za su dinga zuga musu bulalai har sai jikinsu ya dinga jini da tabbai da dama, shafin The Tribe na Facebook ya ruwaito.

Tunanin shan bakin dukan da matan su ke sha yana matukar razanar dasu. Amma duk da haka sun rungumi al’adarsu kwarai ba tare da kyalewa ba.

Ana zuga matan yayin da maza su ke dukansu da bulalen katako masu girman gaske.

Juriyar zugi da radadin yayin da su ke rawa da juyi a gaban jama’a na nuna kauna da rikon amana ga mazajensu na aure da ‘yan uwansu.

Hakan yana kara sanyawa maza da dama su dauki mace da muhimmanci ko bayan an kammala bikin.

Kabilar Dinka: Mace na shekaru 4 ba tare da fara girki a gidan miji ba don karantar halayensa da dabarun zaman aure

Yau za mu baku labari akan kabilar Dinka da kuma yadda su ke aiwatar da aurensu. Duk da sadakinsu yana kai shanu 100 zuwa 500, ana bai wa mata muhimmancin kwarai, Arewa Genius Hub ta ruwaito.

Idan namiji yayi aure, matarsa ba za ta fara girki ko shara ba har sai ta kwashe shekaru 4. Ana kiran wannan lokacin da “Anyuuc” (wato yiwa amarya maraba).

Amarya za ta huta ne tare da kwantar da hankalinta don fahimtar mijinta da kuma dabarun zaman aure.

A wannan lokacin, ‘yar uwar mijinta ce zata dinga yi mata girki, wanke-wanke, debo itace, diban ruwa da kuma sauran ayyuka.

Bayan shekaru 4, mijinta zai shirya babbar liyafa wacce suke kira da “Thaat”, inda za a yanka shanu 3 da awaki 5 don matar ta fara yiwa dangi girki.

Amma idan har mijin yayi wani laifi ko kuma hali mara kyau cikin shekarun nan, matar za ta iya tserewa ba tare da ta biya mijin komai ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe