24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

An aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mata 3 a Iran bisa halaka mazajen su

LabaraiAn aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mata 3 a Iran bisa halaka mazajen su

Wata amarya mai ƙananan shekaru ƴar ƙasar Iran wacce ta halaka mijin da aka tilasta mata aure tana da shekara 15 a duniya, na daga cikin mata uku waɗanda aka aiwatarwa da hukuncin kisa bisa halaka mazajen su a cikin wannan satin.

Soheila Abadi, mai shekara 25 yanzu, an rataye ta a gidan kurkuru bayan an yanke mata hukunci bisa halaka mijinta akan ‘saɓanin iyali’ a cewar bayanan kotu. Shafin LIB ya rahoto.

An kuma aiwatarwa da wasu mata biyun  hukuncin kisa a ranar Laraba bisa laifin halaka mazajen su.

Kotuna ba suyi wa matan da suka halaka mazajen su adalci a ƙasar

Masu rajin kare haƙƙin bil’adama sun yi iƙirarin cewa kusan duk lokacin da mata suka halaka mazajen su, to ana cin zarafin su ne a gida amma kotunan ƙasar Iran basa la’akari da hakan.

Matan guda uku na daga cikin mutane 32 da aka rataye a ƙasar a cikin satin da ya gabata.

Ana yawan aiwatar da hukuncin kisa a Iran

Hakan na zuwa a yayin da ake daɗa samun ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar, inda aƙalla mutum 251 aka kashe a farkon watanni 6 na wannan shekarar. A cewar rahoton Amnesty International.

Yawan mutanen ya ninka adadin da aka kashe a shekarar da ta gabata a irin wannan lokacin.

Daga cikin mutum 251 da aka halaka, 146 daga ciki masu laifin kisan kai ne, sannan aƙalla 86 masu laifuffukan ƙwayoyi ne wanda bai cancanci hukuncin kisa ba a dokar ƙasa da ƙasa.

Yan sanda sun yi ram da matar da ta halaka mijinta bayan ta gano ya na soyayya da wata budurwa

A wani labarin kuma ƴan sanda sun cafke wata bisa halaka mijinta saboda yana soyayya da wata budurwa.

Wata mata ta na hannun hukuma bayan an kama ta dumu-dumi da laifin halaka mijinta bayan ya bayyana soyayyarsa ga wata matar, kamar yadda ‘yan sandan Texas na Amurka su ka bayyana hakan.

Yayin bayani a ranar Asabar, 7 ga watan Mayu, Harris County Sheriff, Ed Gonzalez ya bayyana yadda aka kama Carin Stewart mai shekary 51, wacce ta bayyana cewa da kanta ta halaka mijinta bayan sun yi hayaniya akan soyayyarsa da wata mata.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe