34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Yajin aikin ASUU: Lakcara ta koma tallar dankali saboda neman na tuwo

LabaraiYajin aikin ASUU: Lakcara ta koma tallar dankali saboda neman na tuwo

Wata lakcara a fannin sadarwa ta jami’ar Uyo, Christiana Chundung Pam ta fara tallar dankali don samun na tuwo, Legit.ng ta ruwaito.

An tattaro yadda lakcarar ta samu aikin koyarwar a shekarar da ta gabata kuma ta ce za ta ci gaba da siyar da dankalin har nan da shekara 5 in har hakan zai taimaka ilimin kasar nan ya gyaru.

Pam ta ce tana zuwa tallar kasuwar Akpan Andem da ke Uyo, a Jihar Akwa Ibom a matsayin hanyar rufawa kanta asiri.

Pam wacce ke sana’ar a kasuwa da cikin gari ta bayyana yadda ta koma gona don taya iyayenta noma yayin da take fatan za a koma daga yajin aikin babu dadewa.

Kamar yadda ta shaida:

“Na yanke shawarar komawa sana’ar siyar da dankali don samun na rufin asiri. Ban dade da fara koyarwa ba don ko shekarar ban yi ba, ban tara kudi ba kawai aka fara yajin aiki.

“Har fara rancen kudade nayi don in samu na cin abinci da biyan haraji. Sannan sai da na ranci kudade don biyan kudin haya don gudun ayi min korar kare.”

Lakcarar ta yi kira ga gwamnatin tarayya akan kawo karshen yajin aikin kungiyar malaman jami’o’in (ASUU). Ta ce dalibai dun shiga matsanancin yanayi saboda dayawa dalibai suna kiranta don jin lokacin da za a koma yajin aikin.

Ta ce burikan yara da dama ya tsaya cak saboda yajin aikin da malamai suka shiga.

Bidiyo: Dalibi ya zage yana kwasar rawa don samun maki 10 daga wurin lakcaransa

Wani malamin jami’a ya umarci dalibinsa ya kwashi rawa akan maki 10, shafin Instablog9ja na Facebook ta ruwaito.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, an ga dalibin a gaban aji yana kwasar rawa yayin da sauran dalibai su ke ihu suna kara masa kaimi.

Kamar yadda aka gani a bidiyon, malamin na tsaye a gefe ba tare da ya sa sauti ba, dalibin ya dinga kwasar rawa yana kurda kafafunsa.

Anga yadda malamin yake gyada kai da alamu rawan ya yi matukar burge shi kuma da wuya idan ba zai ba shi cikakken maki ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe