25.1 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Wata kotun Majistare ta umurci wani mutumi da ya share harabar kotun a yunkurin da ya yi na sata

LabaraiWata kotun Majistare ta umurci wani mutumi da ya share harabar kotun a yunkurin da ya yi na sata
Man sweeping street

Wata Kotun Majistare da ke Ota a jihar Ogun ranar Juma’a ta umurci wani matashi dan shekara 28, Abraham John, da ya share harabar kotun na tsawon kwana daya bisa laifin haurawa da yunkurin yin sata.
Mista John, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, ya amsa laifin fasa-kwaurin shiga da yunkurin yin sata.

An yankewa mai laifin hukuncin shara

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai shari’a A.O.Adeyemi, ya yanke wa mai laifin aikin yi wa al’umma hidima Na kwana daya ba tare da wani zabin tara ba.
Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Insp E.O. Adaraloye, ya shaida wa kotun cewa Mista John ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Yuli, da misalin karfe 11:40 a Ifelodun CDA, Ayetoro Itele, Ota.

Ya fasa gidan don yin sata

Mista Adaraloye ya shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya fasa gidan Popoola Kabiru da nufin yin sata.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 412 na kundin laifuffuka, na dokokin Jihar Ogun, 2006.

Yan sanda sun kama wasu mutane takwas bisa yunkurin sace kaya mallakin gwamnatin Najeriya na kimanin dala biliyan biyu

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta damke wasu mutane takwas bisa zargin yunkurin damfarar gwamnatin Najeriya dala biliyan biyu.
Kamen dai ya biyo bayan koke da wani basaraken yankin Opella ya kai mai suna, Richard David wanda ke karamar hukumar Etsako ta tsakiya a jihar, kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor, ya shaida wa manema labarai ranar Talata a Benin.
Mista Nwabuzor, ya ce wadanda ake zargin a ranar 14 ga watan Yuli, 2021, su ka shaida wa 8David da ‘yan uwansa cewa sun samu takardar amincewa daga gwamnatin tarayya, karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), don kwashe kayan aikin bohol wanda kudin su yakai kimanin dala biliyan 2.
“Kayan sun kasance wanda za a yi aikin ruwan garin Okpella wanda Gwamnatin Tarayya ta bada a yi ƙarƙashin Asusun Man Fetur (PTF).
“Mutanen yankin, ko da suka farga cikin hikima suka hana a kwashe kayan.
“A yayin gudanar da bincike, ‘yan sanda cikin sauki suka gano bakin zaren ta inda daya daga cikin wadanda ake zargin ya fallasa gaskiya,wanda ya kasance ma’aikaci a ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatin tarayya, Abuja.
“Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa ya yi jabun sa hannu wanda hakan ke nuni da cewar shugaban kasa ya amince a kwashe kayan .
“An kammala bincike kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu,” in ji Mista Nwabuzor.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su taimaka wa ‘yan sanda ta hanyar ba da bayanai kan ayyukan bata gari.
Cikin wadanda ake zargin wanda ya ke jami’in ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnati ta tarayya, ya shaida wa manema labarai cewa shi ne ya samo takardar bogi.
Wanda ake zargin ya ce ya samu hadin gwiwa ne da wani injiniya wani kamfani a Benin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe