23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Martanin mahaifin Hanifa kan hukuncin da kotu ta yankewa Abdulmalik Tanko

LabaraiMartanin mahaifin Hanifa kan hukuncin da kotu ta yankewa Abdulmalik Tanko

Mahaifin Hanifa, Malam Abubakar Abdulsalam, ya nuna jindaɗin sa kan hukuncin da kotu ta yankewa makashin ɗiyarsa.

Malam Abubakar ya bayyana cewa yaji daɗin yadda kotu ta yankewa Abdulmalik Tanko da abokin harƙallar sa Hashimu Ishyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Kotu ta yanke hukunci ga makashin Hanifa

A jiya ne babbar kotun jihar Kano, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga shugaban makarantar Nobel Kids Academy and North West Preparatory School, Abdulmalik Tanko, wanda ya kitsa sacewa da kisan Hanifa Abubakar, yarinya ɗaliba ƴar shekara 5.

Kotun kuma ta ƙara yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga  abokin harƙallar Tanko, Hashimu Ishyaku.

Ya bayyana jindaɗin sa sosai

Yau naji daɗi sosai cewa ɗiyata Hanifa, ta samu adalci.

Mun gode ƙwarai da ƙoƙarin da kowa yayi sannan lallai anyi adalci yadda yakamata.

A watan Janairun 2022 ne dai hukumar ƴan sandan jihar Kano ta tasa ƙeyar Tanko, inda ya amsa cewa ya halaka ta maganin ɓera sannan ya binne ta a wani ƙaramin rami.

Bayan hukuncin kisa, ina fatan Abdulmalik Tanko ya mutu ba musulmi ba, Sirajo Sa’idu Sokoto

A wani labarin kuma wani bawan Allah yayi fatan cewa Abdulmalik Tanko ya mutu ba musulmi ba. Sirajo Sa’idu Sokoto ya yi fatan cewa duk da hukuncin kisan da aka yankewa Abdulmalik Tanko, yana son ya mutu ba a musulmi.

Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Sirajo Sa’idu Sokoto ya yi wallafa mai zafi dangane da makashin Hanifa Abubakar, dalibarsa.

Dama an kwashe watanni ana ta faman shari’ar Abdulmalik har ta kai ga a wasu mutanen su na ganin dakyar a dauki matakin da ya dace akan shi musamman ganin daga bisani ya musanta kisan da yayi

Sai dai a jiya, 28 ga watan Yuli ne kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya wanda hakan ya sa mutane da dama cikin farin ciki.

Amma duk da haka wasu suna ganin bai dace ya mutu yana musulmi ba, sun yi masa fatan kafirta kafin a karasa masa hukuncin da yayi daidai da abinda ya aikata.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe