28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Kabilar Dinka: Mace na shekaru 4 ba tare da fara girki a gidan miji ba don karantar halayensa da dabarun zaman aure

LabaraiKabilar Dinka: Mace na shekaru 4 ba tare da fara girki a gidan miji ba don karantar halayensa da dabarun zaman aure

Yau za mu baku labari akan kabilar Dinka da kuma yadda su ke aiwatar da aurensu. Duk da sadakinsu yana kai shanu 100 zuwa 500, ana bai wa mata muhimmancin kwarai, Arewa Genius Hub ta ruwaito.

Idan namiji yayi aure, matarsa ba za ta fara girki ko shara ba har sai ta kwashe shekaru 4. Ana kiran wannan lokacin da “Anyuuc” (wato yiwa amarya maraba).

Amarya za ta huta ne tare da kwantar da hankalinta don fahimtar mijinta da kuma dabarun zaman aure.

A wannan lokacin, ‘yar uwar mijinta ce zata dinga yi mata girki, wanke-wanke, debo itace, diban ruwa da kuma sauran ayyuka.

Bayan shekaru 4, mijinta zai shirya babbar liyafa wacce suke kira da “Thaat”, inda za a yanka shanu 3 da awaki 5 don matar ta fara yiwa dangi girki.

Amma idan har mijin yayi wani laifi ko kuma hali mara kyau cikin shekarun nan, matar za ta iya tserewa ba tare da ta biya mijin komai ba.

Hukuma ta yi ram Amaryar da ta hada kai da mai girkin bikinta wurin zuba kayan maye a abinci, jama’a suka dinga marisa

Hukuma ta kama wata amarya da mai girkin bikin da ake zargin sun hada kai wurin zuba kayan maye a cikin abincin biki , LIB ta ruwaito.

Ana zargin amaryar, Danya Shea Glenny Svoboda mai shekaru 42 da mai girkin bikinta, Jocelyn Montrinice Bryant mai shekaru 31 sun zuba wiwi a cikin abincin baki bisa mugunta.

Bikin wanda aka yi a The Springs Clubhouse da ke Longwood a Florida a ranar 19 ga watan Fabrairu, ya samu halartar baki 50.

Sai dai bakin sun dinga marisa bayan sun ci abinci iri-iri da ke dauke da tabar wiwi.

Yayin da aka tambayi angon, Andrew Svoboda, idan na shi bakin sun san abinda ya ke cikin abincin, cewa ya yi a’a.

Daga bisani aka dinga gwaje-gwaje na kwanuka da kofinan da aka yi amfani da su, inda aka gano suna dauke da kayan maye.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe