
Nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara biyan harajin kashi 12.5 na ayyukan sadarwa a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke shirin kara harajin kaso biyar wanda ya hada da ayyukan sadarwa a Najeriya.
Hukumar sadarwa ta shirya taro
Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da haraji kan ayyukan sadarwa a Najeriya ranar Alhamis a Abuja.
Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ce ta shirya taron.
Za a kara kashi 5% akan wanda ake biya a da
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, za a kara biyar akan kashi 7.5 na haraji da ake biya a da wato VAT, kan ayyukan sadarwa.
Wannan kari ne da aka dade da aiwatarwa
Misis Ahmed, wacce ta samu wakilcin mataimakin babban jami’in ma’aikatar, Frank Oshanipin, ya ce karin harajin kashi 5 dama yana cikin dokar kudi tun shekarar 2020 amma ba a aiwatar da shi ba.
Ta ce an samu tsaikon aiwatar da shi ne sakamakon cudanya da gwamnati da masu ruwa da tsaki.
“Za a biya ne a kowane wata, a ranar 21 ko kafin nan wanda biyan zai zama ko kowane wata.
“Ba a kayyade adadin harajin a cikin dokar ba, domin hakkin shugaban kasa ne ya daidaita kudin harajin kuma ya kayyade kashi biyar bisa dari na ayyukan sadarwar da suka hada da GSM.
Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar dakatar da acaɓa a kwata-kwata a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana duba yiwuwar hana sana’ar acaba kwata-kwata a duk faɗin Najeriya.
Ministan Shari’a kuma antoni janar na ƙasa, Abubakar Malami ne ya sanar da haka ranar Alhamis, jim kadan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa wanda Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta. Jaridar Daily Trust ta rahoto
Bincike ya nuna yadda ƴan ta’adda ke samun kuɗaɗen shiga
Ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa ana amfani da ƴan acaɓa wurin haƙar ma’adanai a ƙasar nan sannan hana acanar zai taimaka wurin daƙile hanyoyin samun kuɗin shigar ƴan ta’adda da ƴan bindiga.
Dangane da ko gwamnati zata duba abinda hana acaɓar da haƙar ma’adanan zai jawo ga talakawan Najeriya da kuma tattalin arziƙi, sai ministan ya kada baki yace gwamnatin tarayya zata fifita buƙatar ƙasa fiye da ta wasu tsirarun mutane.
Da yake na shi jawabin, ministan harkokin cikin gida, Aregbesola, ya an yi ƙoƙari sosai wajen tattara bayanan sirri kafin kai harin da aka kai gidan yarin Kuje, amma ya koka kan yadda aka kasa yin abin da ya dace a kai.
Ya kuma ce tuni aka miƙa wa shugaba Buhari sakamakon binciken na farko-farko, inda ya bayar da tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba za a fitar da cikakken sakamakon da zarar an kammala bincike.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com