Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Sirajo Sa’idu Sokoto ya yi wallafa mai zafi dangane da makashin Hanifa Abubakar, dalibarsa.
Dama an kwashe watanni ana ta faman shari’ar Abdulmalik har ta kai ga a wasu mutanen su na ganin dakyar a dauki matakin da ya dace akan shi musamman ganin daga bisani ya musanta kisan da yayi.
Sai dai a jiya, 28 ga watan Yuli ne kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya wanda hakan ya sa mutane da dama cikin farin ciki.
Amma duk da haka wasu suna ganin bai dace ya mutu yana musulmi ba, sun yi masa fatan kafirta kafin a karasa masa hukuncin da yayi daidai da abinda ya aikata.
Sirajo Sa’idu Sokoto yana daya daga cikin wanda su ka dauki zafi dangane da lamarin inda har yayi wata wallafa wacce ta dauki hankalin mutane.
Kamar yadda ya rubuta a shafinsa:
“Ina yiwa Abdulmalik Tanko Fatan ya mutu ba musulmi ba.”
Wannan wallafar ta tayar da kura, har wasu suna ganin menene yayi zafi da yake wannan fatan.
LabarunHausa ta tsinto wasu daga cikin tsokacin jama’a karkashin wallafar ta Sirajo:
Jabeer Abdullahi yace:
“Subhanallah, wannan kuskure ne,shi musulmi ne laifine yayi ba shirka ba. Kuma Allah Yana iya yafe mai..”
Umar Saleh ya yi tsokaci inda yace:
“Dole sai ka nunawa duniya kai ba a saka a makaranta ba ko kuma an saka ka ki yi. Zamanin Annabiمُحَمَّد ﷺ an kashe wata baiwar Allah sai wani bawan Allah ya aibata ta shi kuma mai gidannamuﷺ ya ce tayi tuban da za a rabawa mutanan madina sahabba’i guda 70 in ban mantaba ya ishesu.”
Muneer Yusuf Assalafy yace:
“Amma kai dabban jahili ne.”
Alaramma Buhari yace:
“Ai ba shirka yayi ba,idan Allah ya ga dama zai iya yafe mai ko kuma yayi masa azaba,kawai muyi addu’a Allah tsare mu daga muguwar ƙaddara a rayuwar mu, ameen.”
Amadu Abdullahi yace:
“In bai mutu musulmi ba kai miye ribarka haba bawan Allah musulmi ba ya hudda musulmi a, musulunci.”
Muslim Mg Bature yace:
“Wallahi kila ma sai ya fika daraja a gurin Allah,, kuma ta yiwu ya rigaka shiga Aljanna.”
Yanzu-yanzu: Kotu ta yankewa Abdulmalik Tanko, makashin dalibarsa, Hanifa kisa ta hanyar rataya
Bayan kwashe watanni ana tirka-tirka a kotu, alkali ya yankewa Abdulmalik Tanko, malamin da ya halaka dalibarsa, Hanifa Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya, Aminiya ta ruwaito.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com