24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Hukumar KAROTA tayi babban kamu, ta cafke babbar mota maƙare da giya a jihar Kano

LabaraiHukumar KAROTA tayi babban kamu, ta cafke babbar mota maƙare da giya a jihar Kano

Hukumar KAROTA ta jihar Kano, ta samu nasarar tare wata motar dakon ƙaya maƙare da giya wacce takai darajar maƙudan kuɗaɗe har N50m.

Kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar, ya bayyana cewa giyar takai kiret 2000 a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Yulin 2022. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

An karrama jami’in da kyautar kudi

Babban darektan gudanarwa na hukumar, Hon. Baffa Babba Dan Agundi, wanda ya tabbatar da kamen ya kuma ba jami’in da ya tare motar tukwuicin N1m saboda ƙin karɓar cin hancin N500,000 domin ya saki kayan.

A cewar sa gwamnatin jihar ta haramta shigowa da shan giya a ilahirin jihar, sannan hukumar sa ba zata saurarawa duk wanda ta samo na shigowa da irin waɗannan kayan mayen cikin jihar.

62e2a5f613c3e
Hukumar KAROTA tayi babban kamu ta cafke babbar mota maƙare da giya a jihar Kano. Hoto daga shafin Linda Ikeji.

Ya yabawa zaƙaƙurin jami’in sannan kuma ya nemi sauran jami’an hukumar da suyi koyi da shi sannan su riƙa la’akari da lafiya da dukiyoyin mutane sannan da jindaɗin jihar kafin wani abu daban.

Tsoron Allah yasa naƙi karɓar cin hancin

Halilu Kawo Jalo, jami’in da ya cafke kayan yace an cafke kayan tare da taimakon masu bada bayanai waɗanda suka sanar da su dangane da kayan.

Mun tare motocin dakon kayan a kan titin Obasanjo suna hanyar zuwa Sabon Gari na jihar. Sun bani cin hanci amma naƙi karɓa saboda na san illar da giya ke haifarwa ga rayuka. Haramun ce sannan kuma ya saɓawa koyarwar addinin musulunci ƙarbar cin hanci, hakan ya sanya nayi abinda ya dace.

Baffa ya kuma yi kira ga al’umma da su goyi bayan hukumar sa domin tsaro da kuma lafiyar jihar.

Wani matashi ya rasa ransa bayan ya shiga gasar shanye kwalbar giya mai madarar sukudaye domin ya ci kyautar Naira dubu N6000

A wani labarin kuma wani matashi ya rasu bayan shiga gasar shan giya mai madarar sukudaye domin cin kyautar N6000.

Wani matasi ya sheka lahira, sakamakon kwankwade wata kwalbar madarar sukudaye cikin mintuna biyu, domin ya cinye gasar yuro goma €10 a wata mashaya a kasar South Africa. 

Wani magidanci da ba’a bayyana sunan sa ba, ya ziyararci wani shago a kauyen Mashamba, a yankin Limpopo, inda ya shiga wata gasa da ake so a ga waye zai iya kwankwade wannan kwalbar da gaggawa

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe