23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Daga fita yawon bariki, ta dawo da tsarabar Kanjamau da tarin TB

LabaraiDaga fita yawon bariki, ta dawo da tsarabar Kanjamau da tarin TB

Wani dan Najeriya ya bayyana yadda ‘yar uwarsa wacce wasu suka dawo da ita bayan kwashe shekaru 6 ba tare da an san inda take ba ta warke daga cutukan da ke damunta, LIB ta ruwaito.

Dan Najeriyan mai suna soltune ya bayyana yadda ‘yar uwarsa ta warke daga cutar Kanjamau da tarin TB.

A cewarsa, ta bar gida shekaru 6 da suka gabata kuma bata dawo ba sai da wasu mutane su ka dawo da ita gida su ka ajiye.

Ya wallafa hoton ta wanda aka dauka ranar da aka ajiye ta sannan ya hada shi da wanda aka dauketa ranar Laraba, 27 ga watan Yulin 2022.

Yadda ta kamu ta cutar

A cewarsa:

“A wannan bayanin da zan yi, ba zan tsawaita shi ba. Kanwata wacce a shekaru 6 da suka gabata mu ka nemeta muka rasa a gidanmu haka nan ta warke daga ciwon da ta samo. Cikin shekaru 6 mahaifina da yayata sun rasu sannan mahaifiyata da sauran ‘yan uwana sun ci gaba da addu’a akan lamarin.

“Bayan mako daya da aurena shekarar da ta gabata, aka sanar da ni yadda wasu mutane su ka zo su ka ajiye ta haka nan. Ga hoton yadda suka ajiyeta su ka tafi.

“Ban yi kuka ba saboda hakan kamar nuna rauni ne; mun dinga addu’o’i. Na tuna yadda na dinga tura wa abokaina hotonta don su taya mu addu’a.

“Bayan makwanni kadan, ta fara tafiya. Wata rana mun je asibiti sai likita ke bayyana mana cewa cutar Kanjamau da tarin TB da take fama da su sun warke.

“Ubangiji ne kadai zai iya yin wannan. Hoton nan na kasa shi ne wanda aka dauketa yau. Kayi imani da Ubangiji don shi ne kadai zai iya warkar da mutum.”

Kotu ta daure wani Alkali bayan an gan shi sau 3 a shekara yana yawo tsirara

Wata kotun koli da ke Ohio ta daure wani alkali tare da dakatar da shi bayan ganinsa a karo na uku cikin shekara daya yana tuka mota tsirara, LIB ta ruwaito.

Scott Blauvelt, mai shekaru 50 yana cikin manyan alkalan yankin tun shekarar 1997, inda aka dakatar da shi saboda ganin yadda yake yawo tsirara.

Tsakanin shekarar 2018 da 2021, an kama shi yana tuka mota tsirara har sau biyar, sau uku a cikin watanni 12 da su ka gabata.

A karon karshe kuma an ga yadda ya haske wata matashiyar mata wanda hakan yayi sanadiyyar kai shi gidan yari.

Dama tun a baya an kama shi da rashin kamun kai a bainar jama’a da kuma tukin ganganci a shekarar 2020, an tilasta masa yin wani shiri na shekaru biyu don horar da shi akan kamun kai, ta yuwu hirarwar bata yi aiki ba.

Yayin da ya amsa laifinsa a wannan makon, an daure shi kwana 14 a gidan yari sannan an dakatar da aikinsa tsawon shekaru 5.

Kotun kolin ta kara da cewa alamu suna nuna cewa Scott Blauvelt ya kamu da cutar tabin kwakwalwa kuma ya nuna nadamarsa akan abinda ya yi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe