27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Yadda likitoci suka mayar da wata budurwa abar tausayi bayan ta kashe N60m

LabaraiYadda likitoci suka mayar da wata budurwa abar tausayi bayan ta kashe N60m

Labarin wata ‘yar shekara 18 da haihuwa ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani bayan hotunanta sun bazu ta ko ina, shafin Unknown Facts na Facebook ya ruwaito.

Bayan ta je likitoci sun mayar da ita yanayin jarumar turai Angelina Jolie, hakan yasa har aka tura ta gidan kurkuku akan tsoratar da jama’a da tayi da surarta.

Cikin watanni kadan sai da likitoci su ka yi mata aiki sau 50. An haifeta a shekarar 1998, kuma Sarah tana da kyau sosai amma ta nemi sauya halittarta.

Amma tunda likitoci su ka yi mata aiki sai hancinta da lebenta ta koma wata halittar ta daban. An rarake kuncinta sannan an bula mata su har sau biyu.

Burin Sarah shi ne ta bayyana a wata siffa ta daban amma aikin ya mayar da ita abar dariya. Kuma mabiyanta sun dinga mamaki tare da kwasar nishadi.

Sai dai daga baya Sarah ta fara motsa jiki inda ta rame sosai. Hakan yasa mabiyanta su ka dinga caccakarta.

Rahotanni sun nuna yadda tsabar yawan aikin da aka yi wa Sarah ya illata halittarta. An samu bayanai akan yadda ta kashe $100,000 don ta sauya surarta.

Likitoci sun bar budurwa da kumburarren goshi bayan ta biya N1.1m don a gyara mata gira

Wani lamari da ya faru a Sydney, kasar Australia ya bai wa mutane matukar mamaki, shafin Aubtu.biz ya ruwaito.

Wata Jessie Carr, matashiya mai shekaru 21, wacce ta yanke shawarar inganta kyawunta ta hanyar inganta girarta ta wani salo da ake kira Fox Eye Thread Lift.

A watan Oktoba, Jessie ta biya $2,000, kusan Naira Miliyan daya da dubu dari wurin inganta girar kuma abin bai yiwu ba.

Bayan kwashe makwanni kadan da kammala aikin, sai ta lura kamar akwai zare a wurin girarta.

Hakan ya sa ta bayyana a dandalin TikTok inda ta yi bidiyo ta na jan kunnen mabiyanta akan yin irin wannan aikin.

Kamar yadda ta ce:

“Wannan shi ne mafi girman danasanin da na yi. Sai dai an cire mata zaren daga bisani.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe