A tarihin ana samun mutumin da ya fi kowa kyau, gajarta, tsayi, ilimi, kwakwalwa, iya ado da sauransu, amma a wannan karon Francisco Domingo Joaquim shi ne mutumin da ya fi kowa girman baki a duniya, Instablog9ja ta ruwaito.
Francisco Domingo Joaquim shi ne dan nahiyar Afirka daga kasar Angola wanda ya kafa babban tarihin a duniya.
Kamar yadda aka tabbatar, gaba daya gwangwanin lemu ya na iya shiga bakinsa ya kuma boye tsaf kamar yadda hotonni su ka bayyana.
A shekarar 2010 masu bincike sun gano yadda Francisco Domingo Joaquim, mai shekaru 28 da haihuwa ya kasance mutumin da yafi kowa katon baki a duniya.
Fadin bakinsa ya kai inci shida da rabi (6.5inches), sannan gwangwani mai girman 330ml yana iya shiga bakinsa, kamar yadda littafin tarihin duniya na Guinness ya bayyana.
Tarihin Mary Ann, matar da ta lashe gasar muni ta duniya
Mary Ann ce matar da ta lashe gasar muni ta duniya inda ta samu makudan kudade bayan jerawa da munana da dama wadanda suka fito daga yankuna daban-daban.
Asali ba mummuna bace, hasali ma ma’aikaciyar asibiti ce, sai dai sakamakon wata cuta da ta same ta, halittar ta gaba daya ta sauya, kamar yadda shafin The Enigma na Facebook ya ruwaito.
Sakamakon sauyin halittar, mutane da dama sun dinga zunden ta inda ta zama abar dariya.
A baya, kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce a asibTarihin Mary Ann, matar da ta lashe gasar muni ta duniyaiti, tana zaune cikin rufin asiri da mijin ta tare da yaran ta guda 4.
Wata rana ta wayi gari tana jin sauyi na daban a jikin ta tare da radadi a fuskar ta. Ashe daga lokacin rayuwar ta zata sauya gaba daya.
Bata san zata zama mace mafi muni a duniya ba
Nan da nan jikinta ya fara sauyawa, kuma cikin kankanin lokaci aka kore ta a aiki sannan mijin ta ya rasu inda ya bar ta da yara 4.
Sai dai Ubangiji ya yi gaggawar kawo mata mafita. Duk da dai ta yi kokarin komawa aiki amma ba a amince da ita ba don gudun yaduwar cutar da ke damun ta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com