
Fashe-fashe da harbe-harbe sun afku a garin Owo na jihar Ondo, inda wasu da ba a tantance adadinsu ba suka samu raunuka daban-daban.
Akwai fargabar cewa za a iya samun mace-mace, amma har yanzu rundunar ‘yan sandan Ondo ba ta tabbatar da cewa an samu asarar rai ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta suna nan a shirye domin kwantar da hankula.
Harbin ya faru ne watanni biyu bayan ‘yan bindiga sun kai hari a cocin Katolika na St Francis.
PREMIUM TIMES ta tattaro cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari kan titin Folahanmin da ke garin Owo a daren Laraba.
“Yan sanda a halin yanzu suna wurin, an kai wadanda abin ya shafa asibiti kuma suna cikin kwanciyar hankali.”
Ƴan bindiga sun halaka wani babban ɗan siyasa a Adamawa
Ƴan bindiga sun halaka wani babban ɗan siyasa a jihar Adamawa. Ƴan bindigan su. halaka mataimakin shugaban majalisar ƙaramar hukumar Song ta jihar Adamawa, Hon. Ishaya Bakano, a gidan sa da safiyar ranar Asabar 23 ga watan Yuli, 2022.
Hukumar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga shafin Linda Ikeji, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, yace ƴan sanda sun samu rahoto da misalin ƙarfe ɗaya na daren ranar cewa wasu ƴan bindiga waɗanda baa san ko su waye ba, sun dira a gidan ɗan siyasar mai shekaru 60, wanda yake a Bannga, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Ya mutu bayan an kai shi asibiti
DSP Suleiman Nguroje ya bayyana cewa da zuwan tawagar ƴan sanda gidan suka tarar da ɗan siyasar kwance male-male cikin jini. An garzaya da shi zuwa asibiti inda aka tabbatar ya riga mu gidan gaskiya.
Yace ƴan sanda a yanzu haka na bin sawun ƴan bindigan da ake zargi.
Ana yawan samun ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga a Najeriya inda suke cigaba da cin karen su ba babbaka. Mutane da dama na cigaba da rayuwa cikin firgici dangane da hare-haren waɗannan ɓata garin.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com