Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana cewa shine wanda ya sanar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari batun barazanar ƴan ta’adda ta sace shi. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
A wani bidiyo da aka saki a ƙarshen mako, ƴan ta’addan waɗanda suka sace fasinjojin jirgin ƙasa a watan Maris, sun yi barazanar sace shugaba Buhari da El-Rufai.
Da yake magana a wani shiri a gidan rediyo wanda wakilin jaridar ya bibiya a daren ranar Laraba, gwamnan yace shi kan shi an gargaɗe shi kan tsoma iyalan gidan sa.
El-Rufai ya daɗe yana kira da ayi ruwan bama-bamai kan ƴan ta’adda
Ya kuma ƙara bayanin cewa a shekaru biyar da suka gabata yasha yin kira kan ayi ruwan bama-bamai kan sansanin ƴan ta’adda a duk inda suke, yana mai cewa hakan shine kaɗai maganin matsalar.
Naji labarin wani bidiyo inda suka yi barazanar sace Buhari da ni kaina. An gargaɗe ni na kula wurin sanya iyalai na. Ta ya zamu kasance a ƙasa da sojoji, ƴan sanda da gwamnatin tarayya amma wasu ƴan ta’adda na barazanar sace shugaban ƙasa?
Idan a baya waɗanda ke cikin gwamnati na tunanin wannan wani wasa ne sannan suna ganin kawai yana faruwa a jihohin Katsina, Zamfara, Kaduna da Neja, yanzu ya zo gida dole mu miƙe muyi maganin waɗannan mutanen.
Wannan shiyasa na haɗu da shugaban ƙasa ranar Lahadi na gaya masa akan waɗannan matsalolin. Na kuma gaya masa dangane da bidiyon domin har zuwa ranar bai ma san da shi ba. Na gaya masa sannan washegari gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya sake tabbatar masa shima yaga bidiyon domin a ɗauki mataki.
Shugaba Buhari ya bayar da umurnin a murƙushe ƴan ta’adda
Shugaban ƙasa ya tabbatar min cewa ya gana da hafsoshin tsaro kwana 3 zuwa 4 kafin haɗuwar mu sannan ya basu umurnin cewa su murƙushe waɗannan mutanen da ƙarfin soji. Muna fata Insha Allah cewa sojoji da ƴan sandan da aka ba wannan umurnin za su gaggauta kammala aikin. Ba sai mun jira har sai ƴan ta’adda sun kawo hari kafin mu mayar da martani ba.
Dole sojoji su bi su duk inda suke suyi maganin su. Maganar gaskiya itace mun damu kan matsalar tsaro amma muna fatan gwamnatin tarayya za tayi abinda ya dace.
A cewar sa.
Bidiyo: Ƴan ta’adda sun yi barazanar ɗauke Buhari, azabtar da fasinjojin jirgin ƙasan Abj-Kd
A wani labarin kuma ƴan ta’adda sun yi barazanar sace Buhari da El-Rufai a cikin wani faifan bidiyo.
Makonni kaɗan bayan tawagar motocin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskanci hari a jihar Katsina, ƴan ta’adda sun yi barazanar ɗauke shugaban ƙasar na Najeriya.
Tawagar motocin ta shugaban ƙasar tana kan hanyar ta ne ta zuwa mahaifar shugaba Buhari, Daura, kafin Sallah.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com