27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Tsabar munin amarya yasa mahaifiyar ango tasa an fasa aure ana tsaka da biki

LabaraiTsabar munin amarya yasa mahaifiyar ango tasa an fasa aure ana tsaka da biki

Wani bikin aure a ƙasar Tunisia ya watse bayan uwar ango ta umurci ɗan ta ya fasa auren amaryar mai suna Lamia Al-Labawi, saboda yawan gajartar ta da muni.

Angon bai taɓa ganin amaryar ba ido da ido

Jaridar Legit.ng ta samo daga Mirror.co.uk cewa angon ya fara ganin amaryar ne a karon farko a wurin taron bikin, inda kawai hotunan ta yake gani kafin zuwan ranar bikin.

Mahaifiyar angon na ganin Lamia ido da ido sai ranta ya ɓaci. Baa bayyana sunan angon ba, sannan haka kuma baa sanar da ranar da aka shirya bikin ba.

Amaryar ta kaɗu matuka kuma tayi baƙin ciki sosai

Cikin baƙin ciki Lamia ta garzaya kafar yanar gizo inda ta koks akan lamarin, tana cewa tayi mamakin matakin da mahaifiyar angon nata ta ɗauka.

Tace shirye-shiryen bikin sun ci mata kuɗi sosai. A cewar Pledge Times, Laima marainiya ce kuma sun haɗu da angon ne shekaru huɗu da suka gabata.

An tafka mahawara kan lamarin

Lamarin ya jawo muhawara sosai a tsakanin masu amfani da yanar gizo. Ga kaɗan daga ciki:

@official_nat8 ta rubuta:

Gaskiya gajerun mata irin mu hakan na ci mana tuwo a ƙwarya. Amma ki godewa ubangiji ya kare ki daga auren ɗan maman sa, da jikinki ya gaya miki.

@iam_richcard ya rubuta:

Meye abinda mata ba zasu gani ba a hannun maza? Ina nufin a wannan gajeruwar rayuwar wacce yakamata ace mun huta kawai mu koma barci oooo.

@skincarealadunni ta rubuta:

Kawai ta kama gabanta saboda wannan alama ce cewa uwar ce zata riƙa juya auren.

Tun bayan mahaifiyar mijina ta fado daki ta tarar muna kwanciyar aure da danta ta daina min magana, Matar aure

A wani labarin kuma wata matar aure ta koka kan yadda mahaifiƴar mijinta ta daina mata magana bayan ta faɗo ɗaki ta tarar suna kwanciyar aure da ɗanta.

Wata mata ta koka akan yadda mahaifiyar mijinta ta dena mata magana bayan ta shiga dakin baccinsu ba tare da kwankwasawa ba, ta tarar da ita da mijinta suna tarayya ta auratayya.

Kamar yadda ta bayyana, lamarin ya auku ne bayan surikarta ta kawo musu ziyara na ‘dan wani lokaci, 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe