31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

ASUU ta gabatar da kudirin dokar sanya idanu ga ‘ya’yan masu hannu da shuni da ke fita kasashen ketare karatu

IlimiASUU ta gabatar da kudirin dokar sanya idanu ga 'ya'yan masu hannu da shuni da ke fita kasashen ketare karatu
asuu officials 1024x678 1

Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta yi kira da a samar da kudirin doka da zai tsara yadda ‘ya’yan jami’an gwamnati ke shiga makarantun da ke ketaren Najeriya.
Shugaban Jami’ar Neja Delta reshen Wilberforce Island Farfesa Kingdom Tombra ne ya bayyana haka a wata zanga-zangar hadin kai da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta shirya a ranar Talata a Yenagoa.
Kungiyar NLC ta gudanar da zanga-zangar ne a fadin kasar domin nuna goyon bayanta ga kungiyar ASUU da sauran kungiyoyin da ke da alaka da harkar a lamarin jami’o’in gwamnati a Najeriya.
“Idan aka yi haka, za a samar da ingantacciyar al’umma ta hanyar bunkasa manyan cibiyoyin ilimi da inganta kudade na tsarin jami’a a Najeriya.
“Wannan gwagwarmayar ba wai adawa da gwamnati ta ke yi ba, a’a ta bangaren ma’aikata da masu mulki ne kuma zamu jajirce akan haka sosai.
“Idan masu hannu da shuni za su je jami’a Daya da Dan talaka, ba na jin za a sake yajin aiki.
“Idan ‘ya’yansu za suyi karatu a Gida Najeriya za su nuna cikakken goyon baya ga tsarin jami’a da kuma manyan makarantun Najeriya,” in ji shi.

Dan tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido ya fita da ajin farko (First Class ) a jami’ar Portsmouth dake birnin Landan3

Mai martaba tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido, tare da mai martaba sarkin Zazzau ambasada Nuhu Bamalli, sun halarci bikin kammala karatun dan tsohon sarki Sunusin, mai suna Mustapha Lamido Sanusi.

Sakamakon da dan sarki Sunusi Lamidon ya samu
An tattara rahoton cewa, Mustapha din ya fita da sakamako ajin farko, wato (first class ) a fannin ilimin tattalin arziki, a wata jami’a Portsmouth dake birnin Landan.

A lokacin bikin, sarkin yayi kira ga yaron da ya kammala digirin, da yayi amfani da ilimin nasa wajen samar da cigaba da tallafawa marasa karfi.

Dalilin neman ilimi , inji sarki Sunusi
A fadar sa, yace babban dalilin da yasa ake yin ilimi shine domin a kyautata gobe, da kuma yin hidima ga al’umma.

Da take nagana a yau, sarkin ya ce, Mustapha din ya yi nuna hazaka da ta daga darajar Najeriya, inda ya kara da cewa, dukkanin dalibai da suke karatu a kasashen waje, suyi Koyi da shi domin su fita da kyakkyawan sakamako.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe