34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

‘Yan majalisar dattawa sunyi barazanar tsige shugaba Buhari saboda matsalar tsaro 

Labarai'Yan majalisar dattawa sunyi barazanar tsige shugaba Buhari saboda matsalar tsaro 

Da suke nuna rashin jin dadin su akan matsalar tsaro, majalisar dattawa sun yi barazanar tsige shugaba Buhari .

Sanatoci sun budewa Ahmad Lawan wuta akan cire matsalar tsaro

Jaridar Politics Nigeria, ta gano cewa a taron majalisar na ranar Talata,  sanatocin sun tambayi shugaban majalisar akan dalilin da ya sa ba’a saka matsalar tsaron a cikin takaddar tattaunawa ta majalisar ba. 

Har’ila yau, ita dai wannan jarida ta bayyana yadda ran ‘yan majalisar ya baci sosai akan shiru da akayi akan barazanar da yan ta’addan suka yi na sace shugaban kasa Muhammadu Buhari El-Rufa’i, da kuma sauran manyan yan siyasar kasa. 

tsige shugaba Buhari
‘Yan majalisar dattawa sunyi barazanar tsige shugaba Buhari saboda matsalar tsaro 

Bayan bude masa wuta, da yan majalisar suka yi akan batun, Lawan din ya karkato, inda ya yarda a tattauna akan matsalar tsaro din amma sai a zaman majalisar na ranar Laraba, kuma a yi shi a bude ga kowa. 

Barazanar tsige shugaba Buhari

“Sai da muka daga wa shugaban majalisar murya kafin ya bari a tattauna akan matsalar tsaron, kuma muka ce masa Idan bai bari an tattauna ba, to sai dai ya fara shiryawa domin fuskantar muradun tsige shugaban kasa, domin kasar babu tsaro “.

Inji wani dan majalisar ya shaidawa manema labarai. 

Rashin tsaro ya taa’zzara a kasa

Wannan ba shine karo na farko da yan majalisar ke barazanar tsige shugaban kasar ba. 

Wannan barazana tana zuwa ne, a daidai lokacin da yan ta’adda ke da zarrar iya kai hari har cikin yankin babban birnin tarayyar Najeriya na Abuja. 

Yan ta’addan Boko Haram, sun farmaki Jami’an sojoji na masu gadin bataliya ta 7 , ranar Juma’a, a yankin Bwari dake garin Abuja, wanda suka  kashe jami’an soji takwas uku kuma suka sami munanan raunuka. 

Harin dai yazo ne dududu bayan sati uku da kai wani hari gidan kurkuku na Kuje dake Abuja din, wanda ‘yan ta’addan suka tseratar da  ‘ yan uwansu da fursunoni da dama. 

Ga kuma sabon bidiyon da yan ta’addan suka saki, wanda a cikin sa wani dan ta’adda yayi ikirarin sace shugaban kasa Buharin.

APC ta bayyana shirin da wasu ‘yan majalisa ke yi na tsige Buhari su maye gurbin shi da Osinbajo

Wasu ‘yan majalisar dattijai na gwamnatin tarayya na shirin tsige Buhari, wata kungiya ta jam’iyyar APC tayi zargin hakan.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, kungiyar ta jam’iyyar APC, ta bayyana wannan shiri da suke a matsayin abu marar yiwuwa, sannan kuma babban laifi.

Haka kuma kungiyar tayi kira da a cire shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Ahmad Lawan, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe