31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda matashi ya halaka mahaifinsa kan rikicin gona a Nasarawa

LabaraiYadda matashi ya halaka mahaifinsa kan rikicin gona a Nasarawa

Mutanen garin Masaka a cikin ƙaramar hukumar Karu ta jihar Nasarawa a ranar Litinin, sun shiga cikin ruɗani da tashin hankali bayan wani matashi ɗan fari Tunde Badejo ya halaka mahaifinsa Badejo Idowu saboda taƙaddama akan gona wacce mallakar iyalan gidan ce.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Tunde ya addabi mahaifin na sa kan ya mallaka mishi wani yankin ƙasar gonan tun sama da shekara ɗaya nan baya.

An bayyana yadda matashin ya aikata wannan ɗanyen aikin

Matar mamacin, Madam Tolani Badejo, ta shaida wa wakilin jaridar yayin da ya ziyarci wurin da abun ya faru cewa mijinta ya roƙi Tunde ya ba shi lokaci domin raba gonar cikin adalci ga dukkan iyalan gidan.

Madam Tolani ta ce:

Tun shekarar da ta gabata yake damun mijina kan maganar gonar, to a ranar Litinin lokacin da suka samu saɓani na ƙarshe, sai ya zaro wuƙa ya daɓa wa mahaifinsa a wurare daban-daban.

Ya daɓa masa wuƙa a kai, wuya, ƙirji, hannuwa da ƙafafu har sai da ya halaka shi. Na nemi ɗauki amma tuni ya tsere.

An miƙa lamarin zuwa ga hukumar ƴan sanda

Ayomide Badejo, ɗa na biyu ga mamacin, ya bayyana cewa tuni suka miƙa rahoton lamarin da ya auku ga hukumar ƴan sanda yayin da aka kai gawar mahaifin su ɗakin ajiyar gawarwaki.

Yan sanda sun kama wani matashin barawo da ya kware wajen satar akwatinan talabijin a otal 

A wani labarin kuma wani matashi ya shiga hannun ƴan sanda bisa kwarewa wurin satar akwatinan talabiji a otal.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Edo, sun damke wani barawo mai suna Ahmed Ibrahim, wanda ya kware wajen satar talabijin ta bango a Otal a jihar. 

An tabbatar da cewa, barawon yana kama daki ne a hotal din, kuma idan ya gama zaman sa sai ya sace talabijin daga dakin ya tafi da ita. 

Haka kuma, an gano cewa barawon ya sace talabijin daga wasu hotal guda biyu. An kama shi da wadansu talabijin guda biyu, yayin da yake kokarin guduwa dasu zuwa Abuja domin ya siyar da su. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe