Wani dalibi dan asalin jihar Kano mai suna Abdul Yassar Yahaya Musa, ya bayyana a matsayin daya daga cikin dalibai hudu da suka lashe gasar dalibai ta kasa wadda kungiyar (National computer society ) suke shirya wa.
Yassar shine dalibin farko da ya lashe gasar a jihar Kano
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Yassar din shine dalibi na farko dan asalin jihar Kano wanda ya lashe gasar, tun farkon fara gasar shekaru 20. Yassar din, dan aji biyu ne na babbar sakandare II ta Day Science, Kano.

Sakataren kungiyar ta (Nigerian Computer Society) reshen jihsr Kano , Malam Lukman Bayero, ya shaidawa jaridar Solacebase, cewa dalibai biyu daga makarantun sakandare 35 sun halacci gasar daliban ta kasa.
” Wannan shine karo na farko da muka sami dalibi daga jihar Kano, wanda ya lashe gasar tsawon she
kara 20″.
Bayeron ya fada
A karshe, tace, za’a baiwa gwarazan gasar kyaututtukan su, a 2 watan Agusta a jihar Abeokuta.
‘Yan sanda a jihar Kano sun chafke wani dillalin kwayoyi na bogi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun yi nasarar chafke wani mutumi da ake zargin dillalin jabun kwayoyi ne mai suna Chibezie Onocha a unguwar Sabon Gari da ke jihar.
An chafke dillalin ne a yayin gudanar wani aikin sintiri
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, in da ya ce rundunar ‘yan sanda ta Operation Puff Adder ta damke wanda ake zargin ne a yayin da jami’an leken asiri suka gudanar da wani sintiri a kan hanyar IBB da ke garin Kano.
Hukumar ta PPRO ta ce wanda ake zargin bai musa ba ya amsa laifin safarar magungunan daga Legas zuwa jihar Kano da kuma makwabtan Najeriya Jamhuriyar Nijar.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com