34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Yadda maza suke basaja wai suna son ayi musa aski kawai don suyi magana da ni, wasu ma gashin su bai isa aski ba

LabaraiYadda maza suke basaja wai suna son ayi musa aski kawai don suyi magana da ni, wasu ma gashin su bai isa aski ba

Wata budurwa mai yiwa maza aski, wadda ta sami daukaka ta hanyar yiwa wasu fitataurari taurari, kamar su Davido da Timaya aski, ta bayyana yadda ta fuskanci halin maza, saboda yadda suke kokarin latsa ta, kawai domin tana sana’ar ta ta aski , wadda maza ne aka sani da yinta. 

Ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da wani wakilin National Daily, inda ta fara bayanin yadda tarihin fara sana’ar tata ta fara, bayan ta tafi daga Legas zuwa Abuja, har ta zama mai aski, duk da mahainciyar ta bata son tayi wannan sana’ar. 

maza
Yadda maza suke basaja wai suna son ayi musa aski kawai don suyi magana da ni, wasu ma gashin su bai isa aski ba

Wannan budurwa mai suna Precious Ogedengbe, ‘yar asalin garin Akoko ce dake jihar Edo, kuma ta Zo Abuja ne domin yin aikin tara kudin karatun ta na jami’a. Ta fara aiki a gidan giya, daga nan ta koma babban kanti ( supermarket ). 

Ta hadu da mai askin maza wanda ya koya mata aski

Daga baya sai ta hadu da wani mai aski, inda nuna masa sha’awar ta ga wannan sana’a, shi kuma sai ya koya mata kuma ya karfafeta. Daga nan sai ita ma ta bude shagon ta na kanta. 

Da ake tambayar ta, akan ko tana jin dadin wannan sana’ar tata, sai ta ka da baki tace,

” Na sha fama da rashin da’a, musamman daga maza, wadanda suke zuwa su fake da yin aski. Wasu sai kaji sun ce, ki zo gida mana ki dinga yi mini aski. Amma saboda ta kware a sana’ar ta, tana gane niyyar kwastoman ta daga maganar sa. 

 

” Mafi yawan wasu mazan bama askin ne yake kawo su ba. Babbar niyyar su ita ce, domin su tamnayeni suna son fita shakatawa tare da ni. Sai kaji suna cewa, kyakkyawar budurwa abar sha’awa kamar ki, ina so kizo gida kiyi min aiki. Yadda kayi min magana, ta haka ne zan auna ko zan yi maka aiki ko ba zan yi maka ba “.

Ta taba yiwa Timaya da Davido aski a gidajen su

Wannan zakakurar budurwa, ta  taba yiwa Davido da Timaya aski a gidajen  su, inda hakan ya janyo mata karin daukaka da farin jini, da kari kwastomomi gami da mabiya a kafar sada zumunta, bayan Davido din shi da budurwar sa ta wancan lokacin Chioma , sun yada ta a shafukan su na sada zumunta. 

A kokarin ta na tara kudin karatun jami’a, yanzu haka tana jami’ar kasa ta NOUN, kuma tana ci gaba da sana’ar ta.

Zaman jiran tsammani: Ban cire ran samun masoyin gaskiya ba, Budurwa mai shekaru 70

Soyayyar wata abace mai ban sha’awa, ga dai wata dattijuwar budurwar nan, mai suna Kamaliza Verena, wacce har yanzu bata yanke tsammanin dandanar gardin soyayya da namiji ba, Legit.ng ta ruwaito.

Tsohuwar budurwar mai shekaru 70 a gaba daya rayuwarta bata taba kusantar namiji ba, sannan bata taba soyayya ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe