34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Shugabancin Kwankwaso zai kawo waraka a Najeriya -Idahosa

LabaraiShugabancin Kwankwaso zai kawo waraka a Najeriya -Idahosa

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP), Bishop Isaac Idahosa, ya bayyana tikitin ubangidan sa, Dr Rabiu Kwankwaso, a matsayin “tafiyar waraka” wacce zata ciro ƙasar nan daga halin ha’ula’in da take ciki.

Kwankwaso zai kawo adalci

A cewar sa, za a samu zaman lafiya, cigaba da kwanciyar hankali ne kawai idan akwai gaskiya da adalci, waɗanda yace takarar Kwankwaso zata nuna hakan. Jaridar The Punch ta rahoto.

Da yake magana a wani shirin talabijin na Channels TV ‘Siyasa a yau’ a ranar Talata, Idahosa yace:

Ina matsayin fasto na shekara 33 sannan ana damawa dani a siyasar coci wacce ke da muhimmanci bayan aikin ubangiji.

Nayi mu’amala da mutane daban-daban daga ƙabilu da yankunan ƙasar nan, wanda hakan wani abinda ake buƙata ne musamman a lokaci irin yanzu a Najeriya inda ba yarda sannan akwai rarrabuwa, hakan ya sanya muka zo da tafiyar waraka.

Muna buƙatar waraka domin samun ƙasar da zamu rayu a ciki, muna buƙatar zaman lafiya domin ba zaman lafiya; ba a tilasta cigaba sannan mun miƙa lamarin mu ga ubangiji ya taimaka mana wurin ƙara ɗanƙon zaman lafiya a tsakanin addinai da ƙabilun duniya.

Za su ba ƴan Najeriya mamaki

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, wanda yayi alfahari kan damar jam’iyyar a zaɓen 2023, yace ƴan Najeriya za su sha mamaki idan aka fara yaƙin neman zaɓe a watan Satumba.

Zamu ba ƴan Najeriya mamaki; yau sun ce ba abu mai yiwuwa bane amma gobe za su taya mu murna. Tuni muka fara neman shawarwari sannan na fara tunkarar yaƙin neman zaɓe wanda zai bayar da matuƙar mamaki ga waɗanda ke da shakku kan abinda zamu iya samu.

Ka bar batun kamfen, fara kulawa da lafiyarka, Kwankwaso ga Tinubu

A wani labarin kuma, Kwankwaso ya shawarci Tinubu kan ya bar kamfen ya kula da lafiyar sa.

Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar NNPP ya shawarci dan takarar APC, Bola Tinubu akan ya mayar da hankalinsa kan lafiyarsa.

Ya yi wannan maganar ne yayin tattaunawa da Reuben Abati na Arise TV a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin, inda shugaban NNPP din ya ce ya kamata Tinubu ya duba lafiyarsa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe