
Wata kotun manyan laifuka a birnin Landan, a ranar Litinin din data gabata, ta bayar da belin Beatrice Ekweremadu, wacce ake zargi da laifin siyar da siyan sassan jiki tare da mijinta, Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya.
An bayar da belin Misis Ekweremedu
Kamar yadda jaridar UK Daily Mail ta ruwaito, kotun da aka fi sani da Old Bailey ta bayar da belin Misis Ekweremadu bisa wasu sharudda masu tsauri amma ta ki bayar da belin mijinta, Mista Ekweremadu, wanda a ke ci gaba da tsare shi a gidan yari.
Ga abinda alkalin ya ce:
“Na bayar da belin Beatrice bisa wasu sharudda masu tsauri amma na ki amincewa da bada belin Ike,” Daily Mail ta Burtaniya ta ruwaito abinda Alkali Richard Marks yana ce.
Kotu ta ki bada belin Sanata Ekweremedu
Foundry Chambers dake wakiltar Ekweremadu a cikin wata sanarwa da ta fitar ta tabbatar da belin da aka baiwa Misis Ekweremadu inda ya ke cewa “An ki amincewa da bukatar belin Ike Ekweremadu a ranar Juma’a amma an ba da belin Beatrice bisa wasu tsauraran sharudda na tabbatar da ta halarci zaman kotu tare da kawar da duk wani abinda zai hana ta halarta ga me da sauraron zaman shari’a da aka shirya gudanarwa a ranar 4 ga watan Agusta 2022 da kuma wacce za a yi a shekara mai zuwa .”
Bugu da kari, an tuhumi wani likita dan Najeriya Obinna Obeta da ke aiki a kasar Burtaniya da laifin hada baki da Ekweremadu wajen safarar wani saurayi zuwa kasar Burtaniya domin cire koda don diyarsu.
A cewar Daily Mail, Mista Obeta ya bayyana a gaban kotun Majistra ta Bexley a ranar 13 ga watan Yuli kuma ana tuhumar shi a karkashin dokar bautar zamani da shirya tafiyar wani saurayi mai shekaru 21 a watan Agusta 2021 zuwa Mayu 2022 don cire sassan jikin sa.
A wani rahoto kuma Rudundunar ‘yan sanda landan sun chafke Ekweremedu da matarsa bisa laifin safarar sassan jiki
Rundunar ‘yan sandan birnin Landan ta gurfanar da wasu ‘yan Najeriya biyu da laifin hada baki wajen safarar wani yaro zuwa kasar Burtaniya domin girbin sassan jikinsa,kamar yadda jami’an tsaro suka bayyana a ranar Alhamis.
Wadanda ake zargin shekarun su da sunan su iri daya dana mataimakin majalisar dattawan Najeriya
Wadanda ake zargin – mace da namiji – wanda shekaru da sunan su yazo iri daya da na tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweremadu da matar sa Beatrice Nwanneka Ekweremadu.
Tawagar tuhume tuhume ita ta kaddamar da bnciken
Rundunar ‘yan sandan ta ce tuhume-tuhumen ya biyo bayan binciken da tawagar kwararrun masu aikata laifuka ta ‘yan sandan Biritaniya ta gudanar tare da bayar da wasu bayanai kan wadanda ake zargin kamar haka:
[A] Beatrice Nwanneka Ekweremadu, mai shekaru 55 (10.9.66) ‘yar Najeriya ana tuhumar ta da hada baki don shirya safarar wani yaro da nufin yin amfani da wani sassa na jikin sa, wato girbin gabobi.
“An kaddamar da binciken ne bayan an sanar da masu binciken laifukan da ake aikatawa a karkashin dokar bautar zamani a watan Mayun 2022,” in ji ‘yan sanda.
Bayanan binciken da aka samu yayi daidai da bayanan sirri na Mista Ekweremadu, Sanata mai ci kuma tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da matar ta.
A binciken Pandora Papers, PREMIUM TIMES ta gano cewa Mista Ekweremadu mazaunin Kasar Birtaniya ne.
An tuntubi mai magana da yawun Ekweremadu, Uche Anichukwu, amma har yanzu bai amsa tambayoyi da aka aika masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Dukansu an tsare su a gidan yari kuma za su bayyana a Kotun Majistare ta Uxbridge a yau,” in ji Met.
PREMIUM TIMES ta tuntubi London Met don ƙarin bayani.
Kamar yadda ake gudanar da shari’ar laifuka a yanzu ba za mu ba da ƙarin bayani ba,” in ji Met.
Yayin da ‘yan sanda ba su bayyana jinsin yaron ba, sun ce “yaron ya tsira kuma muna aiki kafada da kafada da abokan hulda kan ci gaba da tallafawa.”
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com