27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Cibiyar bincike ta gano Wani sabon nau’in zazzabin cizon sauro mai ‘karfi’ a arewacin Najeriya

LabaraiCibiyar bincike ta gano Wani sabon nau'in zazzabin cizon sauro mai ‘karfi’ a arewacin Najeriya
Mosquito

Farfesa Babatunde Salako, Darakta Janar na Cibiyar Nazari a likitance na Najeriya, NIMR, a ranar Litinin ya ce ya gano wani sabon zazzabin cizon sauro mai suna anopheles stephensi a arewacin Najeriya.
Mista Salako wanda ya zanta da manema labarai a Legas yayin bikin zagayowar ranar haihuwar sa da wasu ma’aikatansa suka shirya, ya ce a binciken da aka gudanar na baya-bayan nan ne aka gano.

Cuta ce mai wiyar sha’ani

Ya ce, wannan cuta ce mai tsauri mai wuyar kawar wa kuma ba bu ita a ta yammacin Afirka.
Ya ce wannan wani bincike ne da masu bincike na NIMR suka gudanar, kuma hakan yana da tasiri wajen magance zazzabin cizon sauro a Najeriya.

Ana kokarin samo rigakafi

Mista Salako ya ce a halin yanzu NIMR na kokarin samo alluran rigakafi.
Mun yi nazari da yawa kan alluran rigakafi kuma muna duban ci gaban rigakafin.
“Mun yi bincike da yawa tare da hadin gwiwar kungiyoyi biyar don samar da alluran rigakafin ga duk duniya a Najeriya wanda ya bambanta da yadda ake hadawa
,” in ji shi.
Mista Salako ya ce, manufar ita ce a tabbatar da cewa masu binciken na Najeriya sun samu damar bincike daga farko har karshe domin ganin an samar da alluran rigakafin.
Ya ce “in gobe, aka sami wata sabuwar annoba ko cuta, wadda aka sani ko ba a sani ba, zai yiwu Najeriya ta samar da nata maganin rigakafi”.

Hukumar lafiya ta Kasar Ghana ta kebe mutane 98 da suka kamu da cutar Marburg

Hukumar lafiya ta Ghana (GHS) ta tabbatar da bullar cutar Marburg inda aka samu mutane 2 dauke da wannan cutar, cuta Marburg cuta ce mai saurin yaduwa a cikin iyalai kamar cutar Ebola.
Wannan na zuwa ne bayan samun bullar cutar na farko a yankin Ashanti a ranar 7 ga Yuli, 2022, wanda Cibiyar lafiya ta Tunawa da Noguchi ta kasar ta yi bincike akai.
An aika da sakamakon zuwa cibiyar Pasteur da ke Dakar (IPD) na kasar Senegal, tare da tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) inda aka tabbatar da cutar Marburg ce.
“Majinyata biyun wanda sun fito ne daga yankin kudancin Ashanti – wanda cutar ta yi sanadiyar rayuwar su k da dai ba ‘yan uwa ba ne– alamomin cutar sun hada da gudawa, zazzabi, tashin zuciya da amai. An kai su wani asibitin gunduma a yankin Ashanti,” in ji hukumar ta WHO a cikin rahoton da suka bayar.
Shugaban GHS, Patrick Kuma-Aboagye, ya bayyana cewa mutane 98 da aka gano a matsayin wadanda suka kamu da cutar a yanzu haka an keɓe su, ya kara da cewa “wannan shine karo na farko da Ghana ta tabbatar da cutar Marburg.”
Da yake tabbatar da ci gaban, darektan hukumar ta WHO a Afirka, Matshidiso Moeti, ya ce “Hukumomin kiwon lafiya sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka fara shirye-shiryen yiwuwar barkewar cutar.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe