Sananen masanin nau’ra mai kwakwalwa kuma shahararren mai sharhi kan alamuran siyasa Charles Awuzie, yayi kira ga yan ta’addan ISWAP, da su fadi nawa suke so a matsayin kudin fansar fasinjojin jirgin kasa da suke tsare da su.

Yayi wannan magana ne, martani ga sabon bidiyon da yan ta’addan suka saki, wanda ya nuna yadda suke dukan fasinjojin, tare da gallaza musu.
Yan ta’adda sun nemi kudin fansa
An ruwaito yan ta’addan su na ikirarin sai an biya su kudin fansa, gami da barazanar zasu sace wadansu manyan gwamnati, wadanda suka hada har da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ina jin tsoron kada a manta da su kamar yan matan Chibok
Da yake magana a shafin sa na Facebook, Charles Awuzie din ya bayyana tsoron sa akan yadda ake azabtar da fasinjojin, da kuma cewa kada a manta da su, kamar yadda aka manta da yan matan Chibok. Yace, wajibi ne al’ummar kasa, su matsawa gwamnati lamba domin wadannan mutane su samu su dawo cikin iyalan su.
su fadi nawa suke so
A karshe yace, yan ta’addan su fadi nawa ne suke da bukata, inya so a hada musu ta hanyar yanar gizo, domin su dena azabtar da mutane.
Zuwa yanzu na san ‘yan Najeriya sun gane babban kuskuren da suka tafka na zaben Buhari
Tsohon jami’in soja na daya daga cikin jihohin arewa ya ce rashin shugabanni na kwarai a dukkan matakai ne ke da alhakin hauhawar rashin tsaro a faɗin ƙasar nan, musamman a yankin arewa, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce da shugabanni na gari, dakarun sojin Najeriya zasu iya gamawa da ƴan ta’adda cikin watanni shida idan suna da isassun kayan aiki.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com