31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Hadin Kai:Wani Shahararren Limami Ya Sayi Sabuwar Mota, Ya Kai ta Coci domin neman tabarraki

LabaraiHadin Kai:Wani Shahararren Limami Ya Sayi Sabuwar Mota, Ya Kai ta Coci domin neman tabarraki
FB IMG 16587856619044743

Wani limamin Najeriya da ya sayi sabuwar mota ya kai coci domin neman albarka hakan ya ja hankalin jama’a a kafar sada zumunta na Facebook. A labarin da Muideen Olalekan Olagunju ya wallafa, Limamin wanda ba a ambaci sunansa ba yana zaune ne a garin Ijomu Oro da ke jihar Kwara.


Mabiya su kasance masu Hakuri da Juriya a addini

Hotuna yadda aka shararawa wannan mota albarkar ya yadu a shafin Facebook kamar yadda mutane da yawa suka ce yabawa abinda wannan limami ya aikata,ya nuna juriya da hakuri a addini. Inda Wasu ke ganin cewa ‘yan siyasa ne ke hana ruwa gudu a fannin addini suna raba kan ‘yan Najeriya.
Muideen Wanda ya wallafa labarin ya rubuta kamar haka: “A garin Ijomu Oro da ke jihar Kwara babban limamin garin ya sayi mota ya kai ta cocin Venerable of the Christ Anglican Church da ke garin domin neman albarka, idan ba don siyasa da jahilci ba, Nijeriya ita ce kasa dauke da mutane masu hankali”.

Masu amfani da shafin sada zumunta na Facebook sun mayar da martani

Akeem Adeyemo ya rubuta cewa:
Wasu marasa hankali suna barin shugabannin addininsu suna sauya musu zukata inda suke nuna kiyayya mara dalili ga ‘yan uwansu. Abin bakin ciki ne yadda wasu masu tada zaune tsaye ke tada kura a ‘yan kwanakin nan.”

Omo Adebayo ta yi tsokaci :

Yanda muke a da kafin ‘yan siyasa su dasa ƙiyayya, dacin rai da rarrabuwar kawuna a tsakaninmu.Dole ne dukkan addinan Ibrahim su buɗe zukatanmu.”

Abdjelil Adesola Ya ce:

Abin takaici an dauke mana hankulan mu, Abin da muke da shi shine katon kawuna marasa amfani duk da sunan siyasa! Allah ya albarkaci Najeriya da ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da addini da kabila ba.”

Dole na kalubalanci alamomi uku na musulunci a kotu ; cire rubutun Arabi a jikin Naira, rubutun Kurani a jikin kayan sojoji da kuma saka Hijabi ga mata ‘yansanda – Lauya Malcolm

Lauya dan rajin kare yancin dan Adam , Malcolm Omirhobo, ya kara jadda matsayar sa ta tsaiwar gwamen Jaki akan sai ya ga bayan wadansu alamomi uku na musulunci a alamuran al’umma a Najeriya a gaban kotu.

Kungiyar musulunci ta nemi da ya janye tuhumomin
Wata kungiya da take rajin goyon baya ga addinin musulunci da bin harkokin sa, da aka fi sani da MURIC, ita ce ta bukaci lauya Omirhobo din da ya janye aniyar sa ta kalubalantar rubutun Arabi a jikin Naira, sanya hijabi ga mata ‘yansanda da kuma rubutun Kurani a jikin kayan sojoji, idan dai har shi ba kiyayya yake nunawa ga musulunci da musulmai ba.
Da yake mayar da martani, lauyan wanda aka fi gane shi da shigar sa ta addinin sa na gargajiya, zuwa kotu; ya ce, shi ba zai saurari kiraye-kirayen MURIC din ba, “saboda kyasa-kyasan da yake korafi akan su, na al’umma ne gaba daya, domin a samu dorewar kasar da ba’a fifita wani addini ba domin tabbatuwar Najeriya daya”.

Jawabin lauyan akan tuhumar alamomi ukun na musulunci
” Na gani, kuma na karanta rubutun da MURIC suka yi, ta karkashin shugaban ta kuma shugaban kwamatin amintattun ta mai suna Farfesa Ishaq Akintola, inda suke neman na janye tuhumomi uku da nakeyi, wanda nayi roko da sashe na 10 na kundin tsarin mulkin Nageriya, wanda yake magana akan cire addini a tsarin mulki, wanda kuma ya zama hujja a gareni cewa ba kiyayya nake nunawa ga musulunci da musulmai ba, kuma Ni bama ni da ra’ayin nuna kiyayyar addini.
Alamomi ukun sune kamar haka
Tuhumomi ukun da farfesan yake nufi, sune ;

Rubutun Arabi a jikin Naira, sanya hijabi ga mata ‘yansanda musulmai da kuma rubutun Kurani a jikin kayan sojoji.

” Bazan janye wadannan tuhumomi ba, saboda basa nuna wata kiyayya ga musulmai da musulunci, kamar yadda MURIC suke so su nuna wa musulmai domin su yarda da hakan, tuhumomin suna kare muradun yan kasa ne gaba daya, saboda a sami dorewar kasa daya wadda ba’a fifita wani addini ba, domin cigaban Najeriya “. Omirhobo din ya fada a wani jawabi.
” A kan shiga ta da naje babbar kotu da ita, da kuma kotun koli, banga abin da ya shafi MURIC ba, shiga ta yanci na ne, na tunani, walwala da kuma addini, babu inda aka hana ni, matukar ban shiga hakkin wani ba. In dai kuwa ban shiga hakkin kowa ba, kuma ban taka dokar kasar Najeriya ba, babu wanda ya isa ya hana ni yanci na, koda kotu ce, kai ko da shugaban kasar Nageriya ne”.

“Ina shawartar MURIC da tayi wa’azi akan Soyayya ba kiyayya ba. Ku dena dora musulmai akan sauran addinai da kabilu a Najeriya. Ku dena nuna kin wasu bangare, ku zama masu yakana da bin doka.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe