29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Mu muka tallata gwamnati mai mulki don haka dole mu fito mu fada mata gaskiya – Naburiska ya caccaki gwamnatin Buhari

LabaraiKannywoodMu muka tallata gwamnati mai mulki don haka dole mu fito mu fada mata gaskiya - Naburiska ya caccaki gwamnatin Buhari

Shahararren jarumin masana’antar Kannywood da aka fi sani da Mustapha Naburiska ya magantu akan halin da shugabanni suka jefa al’umma, akan halin rashin tsaro da kuma kuncin rayuwa. 

A cikin salo, irin a nuna takaicin abin da yake faruwa, jarumin ya fara da kalubalantar masu mulki, idan da ace ‘yaya ko kannen su ne suke a cikin irin  wannan hali, yaya zasu ji. Amma ace an kama mutane an boye ana azabtar da su, dukkanin shugabanni kowa yayi shiru ya kasa cewa komai. 

naburiska
Naburiska ya caccaki gwamnatin Buhari

A fadar jarumi Naburiskan, a daidai irin wannan lokacin ne kuma, rayuwa tayi tsada, abinci ma da mutum zai ci, ya gagare shi, an sanya mutane a wani hali, babu ruwa, babu wuta, babu ishasshen tsaro, wanda sai da shi rayuwa zata gudana yadda ya dace,  duk da cewa shugabannin sunyi rantsuwar kare rayukan al’umma da dukiyoyin su. 

Naburiskan ya ja hankalin shugabanni

Ya kara da Jan hankalin masu rike da madafun iko, cewa ba a daji ake yin zabe ba, a cikin gari ne ake yi zabe, kuna anayi ne kadai da kuri’ar mutane, ba ta aljanu ba. 

“Wannan gwamnati, mun bayar da kwakkwarar gudun mawa wajen kafuwar ta, saboda mun yi aiki da kudin mu, da jikin mu wajen tallata manufofin ta. Idan kuwa har mun yarda mun yi hakan, to wajibi ne akan mu Idan munga anayin ba daidai ba, mu fito mu fada, ba domin komai ba, sai domin al’umma su san ana shiga lamarin su, kuma ana jibintar lamarin su, wannan hakki ne na dukkanin yan kasa a karbo musu shi. “

“Ku dubi rayuwa yadda ta zama, ku dubi yadda mutane suke kuka, an mayar da wasu marayu, wasu kuma zawarawa, yara kanana sun shiga kuncin rayuwa. Mu da muke cikin al’umma munfi kowa sanin abin da yake faruwa na halin kuncin rayuwa da al’umma suke cik, amma masu mulki, sun ki shiga cikin lamarin al’umma domin su taimaka musu irin halin da suke ciki, an bar mutane komai ya faru a kan su, shikenan ya faru ya kare? 

“Wallahi sai Allah ya tsayar da duk shugaban da yake da ruwa da tsaki akan tsaron al’umma a ranar gobe alkiyama yayi masa hisabi, daidai da irin halin da al’umma suka tsinci kan su a ciki.” 

Ka bar ganin a cikin tsaro kake wallahi baka cikin tsaro sai ka tsare talaka

” Wallahi, wallahi, mutum yabar ganin yana cikin tsaro; wallahi baka cikin tsaro idan baka shiga cikin lamarin al’umma ba, baka cikin tsaro idan baka tsare dukiyar al’umma da rayukan su ba, ko wanene kai.”

Ya kara da cewa, wannan hali na rashin tsaro, babu wanda ya wuce ya je kansa, tunda har ya ritsa da wadansu, basu tsallakeba, to kai ma da kake ganin kana cikin tsaro, to wallahi baka wuce ya shafe ka ba. 

 “Dole ne mu fadi wannan, babu abin da zamuyi face mu fadi wannan abu, matukar zamu tallata ku muce a zabe ku, to wajibi ne mu gaya muku wannan”. 

Naburiskan ya fada

Ba zamu tallata ku ba

Jarumin ya kara re jawabin sa da buga misali da kiraye-kirayen da ake yi na aje a yanki katin zabe, amma kowa ya ki zuwa. Inda kuma ya fito fili ya shaidawa yan siyasa cewa babu wanda zasu tallata matukar ba’a yi abin da ya dace na kawo wa al’umma saukin bala’in da suke ciki ba.

Na wanke wa jarumai mata bireziyya da dan pant, inji Jarumi Mustapha Naburaska

Fitaccen jarumin barkwanci, Mustapha Naburaska ya bayyana a irin wahalhalun da ya sha a masana’antar Kannywood kafin ya kai wannan matakin da yake a yanzu a wata hira da Arewa 24 ta yi da shi a cikin shirin Gari ya waye inda ya amsa tambayoyi da dama.

A cikin hirar, Naburaska ya bayyana cewa a baya ba ya da wata daraja a masana’antar Kannywood sai dai a aike shi siyo sigari, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe