31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Rashin tausayin Buhari, ko shine Fir’auna iyakar abinda zai yi kenan – Sheikh Bello Yabo

LabaraiLabaran DuniyaRashin tausayin Buhari, ko shine Fir'auna iyakar abinda zai yi kenan - Sheikh Bello Yabo
Screenshot 20220725 1216582

A wani faifan bidiyo da ya bayyana an ji Babban Malamin nan Bello Yabo ya fito ya caccaki gwamnati,inda ya yi kira tare da jan kunne game da matsalolin da ake fuskanta a Najeriya,Musamman ta fukar matsalar tsaro.Ga abinda yace:
Buhari ya kamata kaji tsoron Allah! kaji tsoron Allah ! ko fir’auna iyakaci kenan ,wannan bushewar zuciya ya yi yawa,ka ci amanar mu kasan irin wahalar da mukayi akan ka?ashe kasan busashiyar zuciya gareka bakada imani bakada tausayi.”
“Duk mai imani ba zai bar mutane cikin wannan taskun ba,dan ba ‘ya’yanka bane? Ga mata masu goyo da kananan yara cikin wannan tasku da bala’i kuma gwamnati ta zuba musu ido,wannan wacce irin gwamnati ne’ku jami’an gwamnati ya kamata kuji tsoron Allah zukatan ku sun bushe da yawa to wai ya zaku fuskanci Ubangiji game da bayinsa da kuka zalunta.”
“Kai !Buhari kana musulmi rantsuwa fa kayi da Qur’ani,ace a kama mutane kanada yadda zakayi ka kwato su amma ka ki,”ya ku shugabannin gwamnati kuji tsoron Allah yanzu ya zaku ji idan aka ce wadannan ‘ya’yanku ne da matanku.Yanzu Buhari da ace matar kace aka kama cikin wannan halin ya zakaji?yadda zaka ji haka nan ‘yan uwan wadannan bayin Allah zasu ji,ya kamata ku sani ba a duniya za a dawwama ba.”
“Sannan Manzon Allah S.A.W ya ce”ko wannne ku makiyayi ne, kuma ko wannen ku abin tambaya ne ga abinda aka basa kiwo
“.Furucin malamin ya biyo bayan wani Bidiyo da ‘yan bindigan da suka sace Fasinjojin jirgin kasa kimanin watanni 2 da suka wuce suka saki,in da aka ga ‘yan bindigan na dukan mutanen da suka sace wadanda ba su ji ba basu gani ba.

Ba na sace Mutane kashewa nakeyi”- cewar dan bindiga Aleru

Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Aleru, wanda kwanan nan aka nada shi Sarkin Fulanin Yandoton Daji Emirate (shugaban Fulani a Yandoton Daji) ya fito ya bayyana cewa ba ya sace mutane sai dai ya kashe su.
Nadin sarautar Aleru, wanda shi ne jagoran ‘yan ta’adda a Tsafe da Faskari a jihohin Zamfara da Katsina, ya haifar da cece-ku-ce a fadin kasar nan.
Bayan haka, gwamnatin jihar ta dakatar da Sarkin garin, Aliyu Marafa, wanda shine ya ba wa Aleru mukamin, wanda ya kasance ana nema shi ruwa a jallo a jihar Katsina bisa kashe-kashen jama’a.

An fitar da tukwici ga duk wanda yakawo rahoto

Gwamnatin Katsina ta fitar da tukuicin Naira miliyan 5 kan ga duk wanda ya bada bayanan da zasu cimma a damke Aleru, wanda ake zargi da kashe mutane 52 a garin Kadisau da ke karamar hukumar Faskari a shekarar 2019.
A hirarsa ta farko da yayi da manema labarai, Aleru ya shaida wa BBC cewa ya najin haushin Hausawa da gwamnatin Najeriya.

Mutane na su yi garkuwa ni kuma in hallakar

A cikin wani shirin adana labarai mai taken “Mayaƙan Yan Bindiga na Zamfara” da aka ce za a nuna a ranar 25 ga Yuli, 2022, Aleru ya ce yayin da mutanensa ke garkuwa da mutane, shi nashi kawai kashewa ne.
“Mutane na su sace; Ni kuma in je in kashe,” in ji Aleru.

Ana yiwa Fulani wariya a harkokin gwamnati
Wani na hannun daman Aleru da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa tawagar BBC Africa Eye cewa “ana yiwa Fulani wariya a ayyukan gwamnati da sauran hanyoyin tattalin arziki, kuma sojojin saman Najeriya na kai hari ga Fulani makiyaya da kuma kashe musu shanu. “Ya za ayi ace Fulani su zama marasa kima a Najeriya?” yana tambaya.”
Ya koka da yadda aka rufe hanyoyin kiwo da Fulani suka dogara da su yayin da kasa da ruwa suka yi karanci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe