Bayan ganin wani dan asalin kasar Isra’ila, yana shawagi kusa da dakin ka’aba, shugaban ma’aikatar kula da haramin Makka da Madina, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ya gargadi baki wadanda ba musulmai ba.
Dalilin gargadin shiga cikin haramin Makka da Madinan
Biyo bayan hakan, an kama wani dan asalin kasar Saudiyya, wanda ya taimakawa dan kasar Isra’ila din wanda aka ruwaito cewa dan jarida ne, inda ya shigar da shi cikin birnin haramin Makka.

Hukumar kasar Saudiyyar, sun bayyana tsarkin haraman na Makka da Madina, da cewa wadansu ” jajayen layuka ne,” wadanda babu wani wanda ba musulmi ba, da zai ketara su, ko dan wacce kasa ne shi a duniya.
Hukumar saudiyya data dauki mataki kwakkwara akan masu karya dokar
Sheikh Sudais din ya kara da cewa
“Masarautar itace take da cikakken iko da wadannan haramai masu tsarki, saboda haka duk wani wanda ba musulmi ba, da yake kokarin sai ya karya dokar shiga wadannan wurare, lallai baza’a raga masa ba”.
Sheikh Sudais din ya fada
Shugaban ya yi matukar Jan kunne akan kewayawa karya wannan doka, da kuma nuna mahimmancin bin dokar.
Kasar Saudiyya ta damke mutumin da ake zargi da taimakawa dan jaridar kasar Isra’ila shiga garin Makka
An kama wanda ake zargi da taimakawa wajen shigar da dan jarida da ba musulmi ba cikin birnin Makkah mai tsarki, wanda hakan ya sabawa dokar haramta wa wadanda ba musulmi ba shiga garin.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com