26.3 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Ƴan bindiga sun halaka wani babban ɗan siyasa a Adamawa

LabaraiƳan bindiga sun halaka wani babban ɗan siyasa a Adamawa

Ƴan bindiga sun halaka wani babban ɗan siyasa a jihar Adamawa. Ƴan bindigan su. halaka mataimakin shugaban majalisar ƙaramar hukumar Song ta jihar Adamawa, Hon. Ishaya Bakano, a gidan sa da safiyar ranar Asabar 23 ga watan Yuli, 2022.

Hukumar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga shafin Linda Ikeji, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, yace ƴan sanda sun samu rahoto da misalin ƙarfe ɗaya na daren ranar cewa wasu ƴan bindiga waɗanda baa san ko su waye ba, sun dira a gidan ɗan siyasar mai shekaru 60, wanda yake a Bannga, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Ya mutu bayan an kai shi asibiti

DSP Suleiman Nguroje ya bayyana cewa da zuwan tawagar ƴan sanda gidan suka tarar da ɗan siyasar kwance male-male cikin jini. An garzaya da shi zuwa asibiti inda aka tabbatar ya riga mu gidan gaskiya.


Yace ƴan sanda a yanzu haka na bin sawun ƴan bindigan da ake zargi.

Ana yawan samun ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga a Najeriya inda suke cigaba da cin karen su ba babbaka. Mutane da dama na cigaba da rayuwa cikin firgici dangane da hare-haren waɗannan ɓata garin.

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani Mai gari da Dansa a jihar Bauchi

A wani labari na daban kuma, ‘yan bindiga sun ɗauke wani basarake da ɗan sa a jihar Bauchi. ‘Yan bindigan dai sun sace mai garin ne tare da ɗan sa a ƙauyen Zira cikin ƙaramar hukumar Toro ta jihar.

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kai hari tare da sace maigarin kauyen Zira, Alhaji Yahya Abubakar da Dansa, Habibu Saleh a karamar hukumar Toro jihar Bauchi. Mai magana da yawun rundunar SP Ahmed Wakil shi ne ya bayyanawa manema labarai.

Ya ce yan bindigar sun auka kauyen ne da misalin karfe 12 na dare a ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da su.
Ya kara da cewa yanzu haka jami’an tsaro sun bazu cikin daji don neman inda aka yi da su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe