
Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Aleru, wanda kwanan nan aka nada shi Sarkin Fulanin Yandoton Daji Emirate (shugaban Fulani a Yandoton Daji) ya fito ya bayyana cewa ba ya sace mutane sai dai ya kashe su.
Nadin sarautar Aleru, wanda shi ne jagoran ‘yan ta’adda a Tsafe da Faskari a jihohin Zamfara da Katsina, ya haifar da cece-ku-ce a fadin kasar nan.
Bayan haka, gwamnatin jihar ta dakatar da Sarkin garin, Aliyu Marafa, wanda shine ya ba wa Aleru mukamin, wanda ya kasance ana nema shi ruwa a jallo a jihar Katsina bisa kashe-kashen jama’a.
An fitar da tukwici ga duk wanda yakawo rahoto
Gwamnatin Katsina ta fitar da tukuicin Naira miliyan 5 kan ga duk wanda ya bada bayanan da zasu cimma a damke Aleru, wanda ake zargi da kashe mutane 52 a garin Kadisau da ke karamar hukumar Faskari a shekarar 2019.
A hirarsa ta farko da yayi da manema labarai, Aleru ya shaida wa BBC cewa ya najin haushin Hausawa da gwamnatin Najeriya.
Mutane na su yi garkuwa ni kuma in hallakar
A cikin wani shirin adana labarai mai taken “Mayaƙan Yan Bindiga na Zamfara” da aka ce za a nuna a ranar 25 ga Yuli, 2022, Aleru ya ce yayin da mutanensa ke garkuwa da mutane, shi nashi kawai kashewa ne.
“Mutane na su sace; Ni kuma in je in kashe,” in ji Aleru.
Ana yiwa Fulani wariya a harkokin gwamnati
Wani na hannun daman Aleru da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa tawagar BBC Africa Eye cewa “ana yiwa Fulani wariya a ayyukan gwamnati da sauran hanyoyin tattalin arziki, kuma sojojin saman Najeriya na kai hari ga Fulani makiyaya da kuma kashe musu shanu. “Ya za ayi ace Fulani su zama marasa kima a Najeriya?” yana tambaya.”
Ya koka da yadda aka rufe hanyoyin kiwo da Fulani suka dogara da su yayin da kasa da ruwa suka yi karanci.
Sama da ƴan bindiga 100 ne suka halarci bikin nadin sarautar shugabansu da aka yi a jihar Zamfara
Sama da ƴan bindiga 100, a ranar Asabar, suka halarci naɗin sarautar wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga mai suna Ada Aleru a matsayin Sarkin Fulani wacce sarkin Yandoto yayi masa.
Ƴan bindigan sun yi gungu wurin halartar naɗin shugaban na su
Mutane a garin Tsafe jihar Zamfara sun ce ƴan bindigan sama da 100 sun halarci naɗin sarautar shugaban na su wacce sarkin Yandoto yayi masa.
Wata majiya ta bayyana cewa:
Ƴan bindigan sun taho akan babura ba tare da bindigun su ba, ƙaramin biki ne wanda mutane ƙalilan suka halarta.
Sarkin Yandoto, Alhaji Garba Marafa, ya ba da sarautar Sarki Fulani ga ƙasurgumin ɗan bindigan wanda yake kai hare-hare a jihohin Zamfara da Katsina saboda yana son ya rungumi yin sulhu.
A wani zama da akayi, Ada Aleru, ya yarda ya daina kai hare-hare ga mutanen ƙauyukan dake a masarautar. Ya kuma yarda ya bar mutane suje gonakin su.
Hakan ya sanya masarautar tayi naɗin sarautar ga Aleru, domin taimakawa wurin ganin zaman lafiya ya dawo a masarautar.
Naɗin sarautar da akayi wa ƙasurgumin shugaban ƴan bindigan, ya jawo cece-kuce sosai, ganin yadda jihar ke fama da matsalolin tsaro, sannan yana cikin waɗanda aƙe nema ruwa a jallo.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com