23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Bidiyo: Ƴan ta’adda sun yi barazanar ɗauke Buhari, azabtar da fasinjojin jirgin ƙasan Abj-Kd

LabaraiBidiyo: Ƴan ta'adda sun yi barazanar ɗauke Buhari, azabtar da fasinjojin jirgin ƙasan Abj-Kd

Makonni kaɗan bayan tawagar motocin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskanci hari a jihar Katsina, ƴan ta’adda sun yi barazanar ɗauke shugaban ƙasar na Najeriya.

Tawagar motocin ta shugaban ƙasar tana kan hanyar ta ne ta zuwa mahaifar shugaba Buhari, Daura, kafin Sallah.

A wani bidiyo da ƴan ta’adda waɗanda suka ɗauke fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna suka fitar, sun yi barazanar ɗauke da kashe shugaba Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ƴan ta’addan sun bugi ƙirjin cewa zasu tarwatsa ƙasar nan, su kashe ragowar fasinjojin dake a hannun su sannan su siyar da sauran.

Haka kuma a wani faifan bidiyo wanda jaridar Leadership ta fitar, ƴan ta’addan sun bayyana cewa:

Addinin Allah ya riga da ya ta shi kenan, kuma ku baku isa ku gama da Addinin Allah ba, saboda haka mu bayi ne na Allah, muna da tabbacin zai taimake mu.

Kuma ku sani shirin mu ba wai Najeriya bane kawai duniya muka sa a gaba, ka da ku ga wanan aikin (harin jirgin ƙasa) ya ta da muku hankali, daga cikin ayyukan da muka sa a gaban mu wannan bai kai komai ba.

Saboda haka mu kuma muna dogaro ne da Allahu Subhanahu Wa Ta’ala. Duk wani abun da kuke tunanin zaku tanade shi a matsayin zaku yi faɗa da addinin Allah to wallahi ku tanade shi saboda mu mun riƙe Allah.

Yadda muka rayu a hannun ƴan ta’adda tsawon kwana 100 a tsare -Mutanen da aka sako na harin jirgin Abj-Kd

A wani labarin na daban kuma, mutanen da aka sako na harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun bayyana yadda suka rayu a hannun ƴan ta’addan.

Mutanen da aka sako waɗanda harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya ritsa da su a ranar 28 ga watan Maris, sun bayyana yadda suka rayu tsawon kwana 100 a hannun ƴan ta’adda da suka ɗauke su.

Daily Trust ta rahoto cewa bayan sako mutum bakwai daga cikin su a ranar Asabar, akwai sauran mutum 44 ciki har da ƙananan yara da tsohuwa ƴar shekara 85 da suka rage a tsare.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe