29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

 ‘Yan sanda sun kama masu laifi ‘yan daba da barayi har 198 a garin Kano 

Labarai 'Yan sanda sun kama masu laifi 'yan daba da barayi har 198 a garin Kano 

Hukumar rundunar yan sanda ta jihar Kano, tace ta cafke wadansu da ake zargin masu aikata laifuka ne yan daba da barayi har su 198. Laifukan wadanda suka hada fashi, garkuwa da mutane, satar mota, damfara, daba, siyar da mayagun kwayoyi da sauran su. 

Kwamashinan yan sanda ya tabbatar da kamen yan dabar

Kwamashinan yan sandan jihar, Sama’ila Shuaibu Dikko, shine ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da yan jarida, a shalkwatar hukumar rundunar dake Bomphai. 

yan daba
‘Yan sanda sun kama masu laifi ‘yan daba da barayi har 198 a garin Kano 

Kwamashinan yace, dalilin taron yan jaridar, shine domin a sanar da al’umma kamen da hukumar ta yi, da kuma ci gaban da hukumar ta samu, a fadan da take yi da aikata laifuka da masu laifin, kasantuwar kaso na karshe na shekara ya shiga. 

Jawabin kwamashinan yan sanda yayi taron manema labarai

Yace,

” A kokarin da muke, na tabbatar da doka a jihar Kano, mun dada Tsaurara aikin yan sanda, a cikin al’umma, inda muke kai mamaya maboyar masu aikata laifuka, da haramtattun guraren da suke aikata laifuka. Sakonnin sirri da kuma sanya idon yan sanda na keke-da-keke, amsa kiran gaggawa, bin ka’idar aiki, da kuma aiki tare da sauran jami’an tsaro, da kuma jagororin al’umma. ” 

Wadanda aka kama da kayan da aka gano a gurinsu

Ya ci gaba da cewa, a cikin wadanda aka kama din, da akwai yan fashi 42, yan garkuwa da mutane guda 9, yan damfara 16 da kuma yan safarar mutane guda 2. 

Sauran, sune  barayin motici da babura 27, masu safarar kwayoyi 12 da kuma yan daba 92

A fadar Kwamashinan, sauran kayan da aka gano, sun hada da gidan harsashi 25 da bindiga kirar AK47 guda uku, da wata kira micro Uzi guda daya, karamar bindiga pistol guda daya 1, bindiga harbi ka ruga 1 kananan bindigu 10, bindigun mafarauta 9 da kuma ababen hawa 12.

Dikko din ya kara da cewa, sauran kayan sune, Adaidaita 7, babura 3, wukake 122, da kuma sauran makamai masu kaifi da aka kera guda 96.

A karshe ya yabawa jami’an hukumar da shuwagabannin al’umma da ma al’umma baki daya ,saboda hadinkai da suke bayarwa wajen dakile aikata laifuka.

Matar aure ta sa ‘yan daba sun sace ‘yar Adama ta Dadin Kowa, sun yayyanketa saboda tana soyayya da mijinta

Zahra’u Sale, wacce aka fi sani da Adama ta Dadin Kowa ta bayar da labari mai ban tausayi a shafinta na TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Gidan rediyon Premier da ke Kano ma sun kawo rahoton inda suka ce wata matar aure da kawarta sun dauko hayar ‘yan daba sun je sun dauke Fa’iza Ja’afar wacce ‘ya ce ga Adama suka tafi da ita wani kango suka yayyanke ta sannan suka ja mata kunne akan ta rabu da mijin matar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe